[10/10, 3:42 PM] Sadfat: *SANDAR MAKAUNIYA...!* _Sabon Salo._ ©FATIMA SUNUSI RABIU UMMU AFFAN _GAWURTATTU BIYAR TAKU NA BIYU._✌️🔥 *Godiya ta tabbata ga Allah da ya sake bani dama da iko na kawo muku wani sabon labarin sabon takun kuma sabon salo, Allah ka ƙara bani iko da aminci lafiya da basira incigaba da kawo muku gawurtattun labari. Dubun tsira da aminci su ƙara tabbata ga fiyayyen halittu Annabi Muhammad S A W.* _Wannan karon ma labarin ƙirƙirarre ne, da fatan zaku bani haɗin kai domin fahimtar inda ya dosa, sannan ban yadda a juya mini labari ta kowacce irin siga ba ba tare da izini na ba, idan yazo daidai da rayuwarki/ka a rashi ne._ _MASU SO NA ƊAURA MUSU TALLA A PAGES NA LITTAFINA ZASU IYA MAGANA CIKIN FARASHI MAI RAHUSA, MAI TALLA SHI KE DA RIBA 08104335144._ *_Bismillahir rahmanir rahim._* 🅿️ 1️⃣ & 2️⃣ ...Sosai ta ke juyi a saman gadon tana girgiza kai da fizge-fizge kai da ka kalleta kasan tana cikin wani yanayi kuma a hakan idanuwanta a rufe suke kamar mai bacci, cikin wata irin murya mai ɗan ƙara da sauti ake mata magana "Zahra ina sonki kuma har abada ba zan iya rabuwa da ke ba ke tawa ce ni ɗaya." Bin shi take da kallo ta kasa magana shi kuwa ta kowa yake gareta har ya ƙaraso bakin gadon. Zaunawa yayi tare da ɗagota jikinsa ya fara sarrafa ko ina na jikinta, ita dai ga tanan kamar mutum-mutumi ta kasa ko da ɗaga ɗan yatsan hannunta, bakinsa ya saka cikin nata yana tsotsa kamar ya sami lollipop, sun daɗe cikin wannan yanayin a hankali ya ɗago rikitattun idanuwanshi ya ce, "Zahra ke tawa ce har abada." Wani irin haske ne ya bayyana wanda ko idaniyarka ba zaka iya ɗagawa ka kallaba saboda tsananin hasken, bayyanar hasken shi yasa kamar anyi walƙiya sai kuma d'uf!! Ya ɓace kamar anyi ƙiftawar ido. Hasken ne yaci gaba da matsota. A matuƙar hargitse ta farko daga baccin da take wanda in har zata kwanta sai tayi wannan mafarkin, kasancewarta mara tsoro da kuma da kakkiyar zuciya yasata zaunawa akan gadon tana tariyo abin da ya faru *Hisham!* ta kira sunansa kamar yadda ya sanar mata a mafarki, sai ji tayi kamar daga sama an amsa mata _Na'am Zarahta abar sona a ko da yaushe kuma ako wane lokaci ina tare da ke_ da sauri ta fara waige-waige a cikin ɗakin amma ba ta ga kowa ba. Tsuww!!! ta ja tsaki tare da miƙewa, riga da wando ne a jikinta sak na maza domin jeans ne da t-shirt mai kwala irin ta maza kanta hula ce ta tusa gashin kanta ciki, fitowa tayi tsakar gida daidai fitowar Hanne daga ban ɗaki wato mahaifiyarta, kallonta tayi tana hura hanci "Yo Hanne me zan samu ne ko an jiƙa kwakin ne ko yau an sami garau-garau!" Wata harara ta banka mata ta ce"Sannu Baabata kin san dai kowa tasa ta fishshesa akeyi a cikin gidan nan don haka idan kina da kuɗi sai ki saya kici. Zarah ta kalli Hanne da ƙyau ta ce"Allah ko?" Cikin maganar kalar ta maza nigogi. Hanne taja tsaki tare da cewa"Ƙyayi kuma ai" Feesu ce ta shugo cikin shigar ƙananun kaya kan nan nata yasha ƙarin gashi hannunta riƙe da leda, guri ta samu ta zauna da sauri Hanne ta ƙaraso ta ce"Nafisatu sannu da dawowa" Harara ta banka mata ta ce"Yo wanne dare ne jemage bai gani ba? Dole kice min sannu da dawowa Hanne tun da kin ga leda a hannuna kuma yasin kin bar cinshi nima fita nayi aka amfanu dani sannan har na samu na saya." Girgiza kai Zarah tayi ta ce"Matsalar talauci kenan matsiyatan banza kawai ke Hanne ba yanzu kika gama cewa kowa tashi ta fissheshi ba to kema taki ta fishshe ki" cikin maganar nigogi tayi maganar tare da damsewa tayi hanyar waje a hakan babu hijab balle mayafi, tana tafe tana cilla ƙafa yadda dai maza nigogi ke yi. Kai tsaye bakin kasuwa ta nufa gurin da Hajiya Sa'a me sayar da abinci take, tana zuwa ta fara gaisawa da jama'a cikin fara'a domin kowa yasanta da fara'a da sakin fuska take, gurin Hajiya Sa'a ta ƙarasa,ta ce"Hajjaju ya garin?ya yau?" dukkan maganarta ta nigogi maza take yinta. Hajiya ta ce"Zarah yau kin makaro don haka ki koma gaskiya bazan ɗauke ki ba, bayan na sanar miki ƙarfe tara na safe zakizo yanzu fa sha ɗaya ta kusa" Zarah ta ce"Haba-haba Hajjaju aike tamu ce karki ji komai ai ana tare ko ba haka ba?" Ta idasa maganar tana karkata baki da ɗaɗɗa hannu tana yarfewa irin na gayu. Hajita Sa'a ta ce"gaskiya kina cin sa'a ta fa Zarah kije ki mimmiƙawa waɗanda suka saya tukun kafin kici abincin" "Yawwa Hajjaju tamu ina yinki fa a gaskiya ina yinki." Wucewa tayi zuwa cikin rumfar ta fara miƙa musu, zaune ta hangesa cikin kujerar yana murmushi da kallonta, chek ta tsaya tana kallonsa cikin sanyin murya tace" *Hisham!* murmushi yayi ya ce"eh ni ki ƙaraso gare ni masoyiyata!" Waiwayen bayanta tayi babu mai kallonta sai ta girgiza kai kawai ta koma ciki. Har ta kammala aikinta na ranar Hajiya Sa'a ta sallameta sannan ta juya zuwa gida, tana tafe tana daga ƙafa dai-dai wucewarta ta gungun samari matasa ta ce" yah Baaba ya kuke?duka suka d'aga mata hannu da cewa "Lafiya." Wucewa tayi shago zata sayi kayan shayi sai kawai Bala ya ce"daman yanzu mutumin nan ya fita ga abinda ya ce na baki" amsar ledar da Bala ke miƙo mata tayi,leƙawa cikin ledar tayi kayan shayi ne da bread duk dai abinda tayi niyyar saya komai ta gani a fili ta ce"Wai wa?" ya ce"wannan dai da yasa ba bani na baki." bakinta ne taji ya furta *Hisham!* wucewa tayi gida Hanne riƙe da kwalar Musa wato mahaifinsu suna surfawa juna masifa yana cewa "Hanne ki sake ni na wuce" tana cewa"Baka isaba mashayin banza yau sai ka bamu na abinci kai kenan kullum bazaka ciyar da iyalanka ba" Tana shugowa Hanne da Musa suka zuba mata ido Hanne ta sake shi ta ce"Yauwa 'yar albarka sannu da dawo ni nasan Zarah bazata barmu mu kwana haka ba." Wani kallon kwalawa ta mata tace"kika ce me?to kiji da k'yau wallahi kowa ta bisshesa babu ruwa." Tayi shigewarta ciki tana ta6e baki da cewa"sai dai kuyi tayi,Musa kuwa tuni ya fece Hanne ta bisa har ƙofar gida tana masifa shi dai ya samu ya gudu. ***** Wasu ƙyawawan motoci ne jere reras a saman titi kusan guda goma, manyan motoci masu matuk'ar k'yau da tsada gaba da police baya ta police da alamar wani babban mutum ne zai wuce, jama'a sosai sun taru sai d'aga masa hannu suke, shid'in ma cikin fara'a yake d'aga musu hannu, gwamnar jahar Katsina kenan mai ci a yanzu His-Excellency Alhaji Mahmud Mai Abaya gwamna mai k'warjini da kamala haka yayi ta jagaye jama'a cikin sakin fuska yana d'aga hannayensa gefe guda babban d'ansa ne shima tsaye yana d'aga hannu da ka kallesa kasan fara'arsa akan dole yake yinta lokaci-lokaci ya kan d'an ja tsaki domin hayaniyar mutane sosai take damunshj shi mutum ne mara fara'a da rashin son mutane siyasa sam bata ra'ayinsa kamar yarda mahaifin nasa ke burin ganin d'an nasa ya fantsama harkar ta siyasa, a haka dai suka kammala kamfen nasu domin ana gab da fara zaɓe Alhaji Mahmud mai Abaya yana son cigaba da gwamnan sa 4+4 kamar yarda jama'a ke k'aunarshi da haka suka gama, suna komawa gida ya wuce part d'insa yana sakin tsaki wai a kan me mahaifin nasa zai takura masa akan lallai sai ya shiga harkar nan ta siyasa shifa baya son hayaniya ko kad'an burinshi na zama Low ne amma mahaifin nasa yasa shi karantar fannin siyasa domin faranta ran mahaifinsa haka ya daure yayi yanzu ya kammala taya zai sa shi ta dole sai ya shiga siyasaa *Ahmad* Kenan babban d'a a gurin Gwamna mai ci yanzu Alhaji Mahmud mai Abaya." Dafe kansa yayi da ke barazanar tarwatsewa saboda hayaniyar da yasha ta samasa ciwon kai. Hajiya Batula ce ta shugo part d'insa wato mahaifiyarsa cikin shigar alfarma wani d'ank'areran les ne a jikinta tasha make up ta yafa mayafi kalar leshin k'afarta da takalli mai kyau cikin fara'a ta dubesa "My Son Mahaifinka ya shugo fa yana jiranka." d'agowa yayi cikin da kushewar murya ya ce"Haba Mum akan me Dad zai takura min dole sai nayi abinda bana so Nifa Siyasa bata cikin ra'ayina." Zaunawa tayi tare da d'ago kansa ta d'aura saman cinyarta cikin taushin murya ta fara magana"My Son ina son kayi hak'uri kaso abinda mahaifinka ke so nan gaba zaka ga amfanin hakan, kace ni na fad'a maka." Cikin damuwa yace"Mum bana son damuwa ne da nuna hamaiya irin ta siyasar k'asar mu" ,ta ce"Weldone *Ahmad* karka damu in sha'Allahu siyasa Alkhairi ce a gareka." Murmushin yak'e kawai yayi, tare da mik'ewa ta kama hannunsa suka fita." ***** Zarah ce zaune tana kallon Yayarta Feesu da Hanne suna fad'a dai-dai shugowar Habu, hannayenshi rik'e da adda da sanda domin riƙaƙƙan ɗan daba ne. Kallonsu ya ke wani irin a shawu yana rangaji saboda shaye-shayen da yake na wiwi da taba sigari, Feesu cikin rashin kunya da fitsara ta ce "Wai kai Habu mene ne haka zaka shugowa mutane ko sallama babu?" Ɗago jajayen idanuwansa yayi ya ce"Ke wallahi yanzu zan sassara miki jiki, idan kika nemi ki mini rashin kunya, ni tsaranki ne?" Tsaki taja mtsuww!!! Zata wuce ya jawota da ƙarfi har sai da ta faɗi ya ɗaga wuƙa zai sara mata, sai ganin Zarah aka yi ta riƙe hannunshi da ƙarfi don har Feesu ta sadaƙat. Ta ɗauka shi kenan ta mutu, da ƙarfi ta saki ƙara jin shuru yasa ta buɗe idanuwanta sai ganin Zarah tayi riƙe da hannun Habu cikin zafin nama. Da sauri Feesu ta tashi daga ƙasan da ta faɗi duk da haka bakinta bai mutu ba ta ce"Wawa jaki kawai." Zarah ta ce cikin irin maganarta ta maza "Haba Baaba meye hakan kai sai kace ba namiji ba ai ba a biyewa mata." Cikin maye da maganar mashaya ya ce"Ai da kin barni na koyawa 'yar iska hankali tun da bata da kunya." Hanne ta ce"Ku dai yaran nan dukanku babu na ƙwarai, ni da Musa mun haifi bala'i yanzu daga mashayi sai karuwa sai ke Zarah da muka kasa gane kan ki macece ko namiji. Gaki nan dai sai kace mai *Ruhi biyu*" Zarah ta ce"Ai kun fini sani tun da ku kuka haife ni, kuma abu a duhu ina jin dai Ruhi buyu ne a jikina. Sannan yadda kika ce mu bala'i ne kuma bala'in kan ku ne chen da yawarki Hanne." Ta wuce tana kaɗa ƙafa da bonsin irin na gayu. Kasancewar magrib ake kira alwala tayi ta fara sallah bayan ta idar fita tayi da chenjinta gurin Bala mai kanti don juice da biskit zata saya taci ta kwanta saboda dare kuma rishonta babu kalezir bare ta dafa indomie. Tana shiga ya ce"Yawwa Zarah kamar kin san yanzu nake cewa zan aika miki don saurayin nan naki ya bani na baki." Kallonshi take bakinta a sake kafin ta miƙa hannu jiki a sanyaye ta amsa Juice ne da biskit kamar na yadda zata saya. ta ce"Amma Bala me yasa idan yazo baka kirana sai ya tafi." Murmushi yayi ya ce"Na sani ko lokacin baki gida karna aika baki nan." Juyawa tayi tana faɗin "To na gode" Bayan ta koma gida sallar isha'i tayi sannan ta zauna bakin ƙaramin gadonta ta ciro ta faraci. Feesu ce tsaye ke shirinta cikin ƙananun kaya riga da wando tayi matsu sosai, ta feshe jikinta da turare sannan ta ɗauki jakarta tayi hanyar fita. Zarah ta ce"Feesu wai ke kullum kina hanyar fita baki zama gida ki kwana." Wani kallo ta mata kafin ta ce"To idan ban fita na nema ba kece zaki ciyar dani? Kina jin dai iyayenmu da kansu suka ce ko wacce ta fita ta nema ta ciyar da kanta to akan me zan zauna da yunwa gara naje na sami abin da na sama cikina." Tana kaiwa nan ta fice gyara kwanciya Zarah tayi tana cewa"Bazan biye miki ba gara na kwanta ƙarfe tara Hajjaju ta ce na fita ke ce gantalalliya. Kamar kullum cikin barcinta ta fara jin mutum kusa da ita, *Hisham* ta kira sunansa cikin cool voice kallonta kawai yake yana murmushi ta ce"Please kai waye me kake nema a gurina? Zaunawa yayi kusa da ita tun da take ganinsa a mafarki bata taɓa iya masa magana ba, wannan maganar da tayi ma a zuciyarta tayi sai dai ga mamakinta sai ji tayi ya ce"Zarahta a sannu zaki gane ko ni wane ne, abin da kawai nake so da ke kisa ni a zuciyarki karki bari wani ya ce zai raɓeki shine babban kuskure da zai yi a rayuwarshi" kallonsa kawai nake ko kiftawa babu gashi ko yatsana na kasa d'agawa magana nake son masa na kasa,d'agoni yayi juwa jikinsa sannan ya ce"Duk wani abu dake zuciyarki na sani nasan kina da tarin tambayoyi gami da ni lokaci shi zai nuna hakan zaki san koni waye" had'e fuskarsu yayi guri guda tare da zaro harshensa yana lasar hancinta zuwa cen ya sauka a bakinta ya fara tsotsa a hankali har izuwa wiyanta. Magana take son yi amma ji take kamar an d'aure mata harshenta, gangarowa yayi wuyanta yana lasa, k'ara ta saki da k'arfi tana kurma ihu dai-dai shugowar Hanne tana cewa "Lafiya?" Jin muryar Hanne ta bud'e idanuwanta a hankali rana ce ta kashe mata ido,ajiyar zuciya ta saki ganin har gari ya waye,tsohon agwogwonta ta kalla ganin goma saura ta tashi a furgice wanka tayi tare da sallah sannan ta fice,tana zuwa Hajiya Sa'a tace"wallahi Zarah baki isa ba,ni bazan iya ta bauta dake ba bayan ke baki min abinda nake so ce miki nayi tara na safe zaki dunga zuwa yanzu har goma da kwata,gyara tsayuwarta tayi tare da yarfe hannu tace"kin san dai bamu haka dake Hajjaju." "Daga yau sai mu fara." Hajiya Sa'a ta fad'a tana ci gaba da aikinta,juyawa Zarah tayi ba tare da ta sake cewa komai ba,har tayi d'an tafiya taji Hajiya Sa'a ta saki k'ara domin gama d'aya tukunyar girkinta ta 6are lokaci guda kamar an ture,ko da Zarah ta juyo ta gani murmushi tayi tare da bonsiwa tace"an gaya miki ni d'in tawasa ce,kawai ta wuce amma har cikin ranta take mamakin ya akayi tukunyar ta turgud'e ta6e baki tayi tare da d'aga kafad'a irin ko a jikinta d'in nan." Tunani take ina ya dace taje ta fara wani aikin domin dole ne tayi inhar tanason taci abinci don idan zata zauna babu aiki ba ruwan Musa da cinta bare Hanne,ji tayi kamar an d'agata sama sai ganinta tayi tsaye bakin gidan wani abinci na masu kud'i duk wanda zajaga yazo gidan abincin nan to wani k'usa ne a k'asar nan domin na manyan mutanene,hango ma'aikatan gurin tayi kowa da uniform d'insa gaba da bayanta ta kalla ita sam bata san ma ina ne nan ba." 08104335144 _Somin taɓi kenan, taɓa ka lashe._ [10/10, 3:49 PM] Sadfat: *SANDAR MAKAUNIYA...!* _Sabon salo._ _GAWURTATTU BIYAR TAKU NA BIYU._✌️ *UMMU AFFAN*🤏 🅿️ 3️⃣ & 4️⃣ ...Tunani da tambayar kan ta take ta shiga ko ta tsaya? Ganin irin motocin da ke shige da fice a gurin yasa ta ji a zuciyarta kamar idan ta je ma korota za a yi, sai kawai ta ji zuciyarta na hankad'ata ita dai bata san yadda a ka yi ta shiga ba sai ganinta tayi a ciki. Gurin shugabar wajen ta nufa tun kafin tayi magana matar cikin fara'a ta ce, "Ƙwarai ke ce daman Yayanki yazo tun d'azun ya sanar min ina ganinki na gane ki, domin sak ya zayyano min yadda ki ke." Murmushi ne ya suɓucewa Zahra ita dai ba tasan ko na miye ba, nan matar ta fad'a mata aikinta a wajen kai wa kostomas abinci da tambayarsu abin da suke so. Zahra tayi godiya sannan ta sanar da ita albashinta tare da bata uniform ta ce"Kije gida gobe sai ki dawo" Mik'ewa tayi"To na gode." Da haka ta fita wajen tana ta waige-waige." .............................. Alhaji Kabiru Tafida shine d'an takara a babbar jam'iyyar hamayya ta PRP babban attajiri mai ji da dukiya da sarauta domin jinin sarauta ne shiyasa yake da *IZGILI*(Sunan book d'ina)da k'asaita mutum ne mai nuna mulki da d'agawa jinin sarauta ne amma Allah ya d'aura masa k'aunar siyasa ya shiryayin gwamnar jahar Katsina ko ta halin k'ak'a,tare sukayi da kara da ANPC Jam'iyar dake mulki a yanzu inda Alhaji Muhmud Mai Abaya ya kayar da shi da k'uruk'u masu dama,shiyasa a wannan karon ya shirya sosai domin sam baya son gwamnati mai ci tayi 4+4 burinsa ya tuntsirasu da k'asa koda ta hanyar satar k'uri'a, domin tuni suka shiryawa hakan ta hanyar shiga gidajen talakawa a kai musu kayan abinci bai wuce taliya kwaya da'aya da makroni d'aya da su maggi da bai wuce na nera hamsin ba sannan omo shima hakan da musu dad'in baki akan inhar suka dangwalawa jam'iyar PRP zasu sami abubuwa da dama,wanda shi kuma Alhaji Kabiru Tafida ba wannan ne a cikin zuciyarsa ba shi dai hangen mulki yake ta hanyar da zai tara kud'i da kuma mulki domin yanzu siyasar tamkar kasuwanci wasu daga ciki suka d'auketa." Tsaye suke tare da gungun matasa 'yan bangar siyasa Alhaji Kabiru Tafida ya ce"Abin da nake so daku shine ku shirya gobe zamu fita yak'in neman zaɓe,sannan naji wancen banzan gwamnan Mai Abaya wai yau zai fita, ina son ku ta da musu hankali kar a sake abarsu suyi cikin lafiya, Ihuww suka saka Habu ne mai cewa"sai kai babba d'an gidan babba ba gudu baja baya ko ank'i ko anso sai ka lashe indai muna tare da kai sai kaci,murmushi kawai yake domin yana son yaji ana masa kirari nan ya ce"A bashi dubu goma" Ai Habu jin haka nan ya k'ara d'aga murya da kirari. da haka suka koma ciki, Alhaji Mudi wanda shine idan sun ci yake mataimakin gwamna. ya ce"Ni wai Alhaji Tafida ko kaji wani batu? Kallonsa ya yi da k'yau ya ce, "Wanne batu?" Akan yak'in neman zaɓe da Mai abaya zai fita wai harda babban d'ansa da yake burin shima yayi siyasa,wata dariya ya saki mai k'ara yace"ohh d'an nasa ke son ya gajesa kenan to muzuba mu gani shi babban mutum ma mun iya dashi bare d'ansa yaro k'arami" ya ce"Babban d'ansa nake maka magana d'an nasa fa zaiyi 35y yace"to sai me?ba yaron bane?ko kai baka haifi d'an 35y ba?" ya ce"Haka ne,dafasa Tafida yayi yace"Mudi wallahi kaji na rantse maka ko ta halin k'ak'a sai mun mulki jahar nan tamu son mulki irin na siyasa a jinia yake kuma na rantse da Allah sai nayi,yana kaiwa nan ya tashi ya shige ciki." ........................... "Dad ban san me yasa jikina yayi sanyi da fitar nan tamu ta yau ba, don Allah ko za'a cenja tsari zuwa gobe,dafasa Alhaji Mahmud yayi yana murmushi ya ce"Yarona ka zama gawurtacce mana kasan kuma fa ina burin nan gaba na ga ka zamo shugaban k'asa ba ma gwamna ba, zaro ido yayi fuskarsa da murmushi ya ce"Dad haka kawai naji jikina yayi sanyi bana son wani abu ya faru da kai mu bari gobe mana, ya ce"ba abinda zai sameni sai alkhairi sannan naji labarin gobe Alhaji Kabiru Tafida zasu fita kaga yau ne dai ya dace mu fita,gyad'a kai yayi da cewa"shi kenan Dad bari naje na shirya,cikin jin dad'i da alfahari yace"Allah ya maka albarka ina alfahari da kai yarona,bari nima na isa gurin wad'anda zamuyi gangamin suna waje." Murmushi kawai yayi ya fita,da har zai shiga part d'insa dake cikin gidan domin ya shirya sai kuma yayi tunanin bari yaje gidansa." Gida ne mai k'yau da tsari na 'ya'yan manya hune yayi a bakin gate mai gani yazo ya bud'e masa ya shiga ciki tare da samun guri yayi parking jiki a sanyaye ya fito zuwa cikin gidan, zaune take a parlour taci kwalliya sosai tayi kyau cikin wasu riga da siket da akawa d'inkin wulak'anci gaba d'aya saman nonuwanta a waje suke babu abinda ba'a gani taci kwalliya domin 'yar k'walisa ce ta k'arshe Hafsat kenan mata a wajen Ahmad ko kallon inda take baiyi ba ya nufi hanyar bedroom,kallonsa take cike da mamaki da sakin baki tasanshi yana son ya ganta cikin wannan yanayin to ko lafiya?ta tambayi kanta tashi tayi tabi bayanshi, gani tayi yana kiciniyar cire kaya da alama wanka zai shiga da sauri ta iso garesa tare da rungumesa ta baya gama d'aya nonuwanta a saman bayansa wani yarrr yaji ya juyo da ita ta gabansa a jikinta babu abinda yafi k'auna sama da nonuwanta sa hannu yayi a hankali yana shafasu, kallonsa tayi ta ce" Ahmad lafiya naga ka shugo cikin wani irin yanayi?kasa ce mata komai yayi ya had'a bakinsu waje guda na aika mata da wani hot kiss itanma biye masa tayi sosai suke romancing junansu ganin tsayuwa bazata yuwuba suka isa bed sosai yake ya mutsata son ransa kamar yadda ita ma take masa sun d'auki tsawon lokaci a haka wayarsa ce tayi k'ara sai lokacin hankalinsa ya dawo jikinsa d'aukar wayar yayi ganin sunan Dad da sauri ya watstsake ya d'aga, muryar Dad yaji yace" *Ahmad* kana ina ne kai fa muke jira, da hanzari ya ce"Dad ina zuwa yanzu in sha Allah,da sauri ya saki Hafsat ya fad'a bathroom ita kuwa binsa tayi da wani mayen kallo gaskiya a yadda take mayyar Sex idan har Ahmad bai kusanceta ba akwai matsala tashi tayi cikin wani irin mayen yanayi ta bisa bathroom d'in. Bakin k'ofa ta tsaya ta zuba masa rikitattun idanuwanta,kallo d'aya ya mata ya kaida fuska yaci gaba da wankansa,bayan ya gama tawol ya d'aura yazo ya ra6ata ya wuce,tasan halinsa duk domin kallon da ya mata ta san abinda yake nufi,jiki a sanyaye ta dawo bakin bed ta zauna tana kallonsa har ya gama shirinsa cikin manyan kaya wato d'inkin shadda har da malum-malum tuni daman duk wata shigar k'ananun kaya ya dena sai lokaci zuwa lokaci saboda girman nan da mahaifinsa ya k'ak'a ba masa,sai da ya gama saka turarensa sannan yazo ya shafa gefen fuskarta murya cen k'asa yace"am sorry dear sai na dawo,ji tayi kamar ta kamosa jikinta haka ya fita ya barta cikin wani irin yanayi,tun farko shi ya sabar mata gashi yanzu jar tana neman ta fishi jaraba jinta tayi cikin wani felling sosai,a hankali tasa hannu k'asanta tana d'an murjawa a hankali tana sakin 'yar k'ara ganin hakan bazai mata ba tashi tayi ta shiga bathroom ta tara ruwa ta shiga ciki tare da bud'e k'afafunta sosai take jin kewar mijin nata ita macece mai son sex da soyayya duk da mijin nata ya koyar da ita amma yanzu jarabarta tafi tasa bata iya shige-shige ba duk jarabarta akan mijinta take k'arewa sai dai yau ji take kamar me ji take idan namiji bai kusanceta ba akwai matsala,ta dad'e cikin ruwan sannan ta fito d'aure da tawul tana goge jikinta shiryawa tayi cikin wasu shegun kaya sosai suka mata kyau fitowa tayi parlour 'yar aikinta ce ta kawo mata abinci amsa tayi tanaci a hankali tana tunanin mijinta,wayarta ta ciro tare da danna kiransa,lokacin kuwa sosai suke cikin jama'a domin saboda hayaniyar mutane sam baiji kiran nata ba,ta kira har sau uku daga k'arshe cilla wayar tayi ta fara hawaye cike da kewar mijin nata,acen kuwa taro yayi taro sai gudanar da al-amura suke yadda ya kamata,mutane sosai suka taru suna d'aga hannu ga kalandun gwamna Alhaji Mahmud mai abaya nan ta ko ina an lik'a wasu yanzu ake lik'awa abin nasu yayi kyau sosai mutane ke k'aunarsa saboda tausayin talakawansu,cikin sauti na sifik'a yake magana"jama'a da farko Assalamu alaikum." Gaba d'aya suka amsa sannan ya ci gaba da cewa"kamar dai yadda kuka sani wannan jam'iya itace mai mulki a jahar nan harma da k'asar nan,muna so kuci gaba da bamu goyan bayanku kamar yarda muka faro ga sauran aiyuka namu da bamu kammala ba insha'Allahu da zarar anyi za6e zamuci gaba da aiyukanmu." Ihuww aka saka ana tafa masa wasu nace"gwamna sai kayi gwamnanmu sai ka sake." yace"to madha Allah mudai wannan jam'iyya tamu cigaban talakawa shine takenmu domin samawa matasanmu aikinyi,tafi tafff-tafff-tafff ake,wani ne ya amsa sannan gwamna ya koma gurin zamansa,mutum da k'arfi yace"ANPC,Jama'a suka amshe da "Nasara chenji."ANPC."Nasara chenji."ANPC.Nasara chenji,sannan yaci gaba da bayaninsa,ana cikin haka saiga 'yan ta'adda bangar siyasa,sune suka fasa taron inda suka fara sare-sare nan fa kowa yayi takansa sosai ran gwamna ya 6aci da wannan abun kuma yasan 'yan babbar jam'iyyar hamayya ne suka turo,amma dai yasan duk siyasa ne da hamayya hakan yasa dai kowa ya watse inda akabar nasun 'yan bangar suka had'e da juna. Su kuwa tuni suka wuce ran Ahmad ya ɓaci sosai wai a hakan mahaifin nasa ke son ya fad'a harkar gadan-gadan? .............................. Zahra ta fara zuwa aikinta wannan gidan abinci na masu kud'i, ba laifi tana samu sosai hakan yasa idan ta kwashi albashi tana sayawa Hanne kayan abinci Shinkafa da garin tuwo sai kwaki da su maggi tace tayi cefane, ita kuwa daman idan ta karya da shayi da breadinta idan taso har kwai take toyawa sannan ta wuce acen take cin na rana da sunce idan tanaso zata iya kwana amma tace"a'a tafi so ta dunga kwana a gida hakan yasa da yamma ta ke komawa gida wataran ma harda abincinta take tahowa,idan tayi niyya ta d'ibarwa Hanne tunda Feesu daman ba gida take kwana ba,yau a gajiye ta dawo wanka tayi tare da d'auro alwala jin an fara kiran sallar magrib mai ta shafa da yake daman ita mai kawai take shafawa wataranma bata shafawar don komai nata na maza ne,sallah ta farayi sannan ta jawo take away d'inta ta faraci babu abinda k'irjinta keyi sai bugawa,ta rasa dalili amma saboda da kakkiyar zuciya irin tata ko gezau babu alamar tsoro a tattare da ita,bayan ta gama tashi tayi ta fita jin ana kiran sunanta *Zahra!* *Zahra!!* *Zahra!!* inda take jin sautin kiran take bi har zuwa d'an katin Bala, chek!!! ta tsaya ganin Hisham a bakin k'ofar da alamar Balan ya tafi, don shagon a rufe yake, babu abin da yake sakar mata sai murmushi, Aljani ne ko mutum? Ta tambayi zuciyarta sai kuma ta d'aure fuska sosai tare da cewa"Waye kai?." har lokacin murmushi ne kwance a fuskarsa ta kowa yayi har zuwa inda take ita kuwa ko gezau tana a tsaye bata matsaba har ya k'araso cikin very sweet cool voice ya ce da ita"Har yanzu lokaci bai yi ba,da sannu zaki gane Aljani ne ko mutum, nazo gurinki na tayaki hira ne idan babu damuwa?" Juyawa tayi da niyar komawa gida,sai taga wani siririn mutum da kwala-kwalan ido da k'aton kai harda k'aho,sake juyowa tayi ta kallesa har lokacin ita yake kallo fuskarsa da murmushi ya k'ara takowa gareta tare da rik'e hannayenta sai taji sam ta kasa kwacewa,yasa hannu yana shafa fuskarta yace"ke tawa ce ina so ki soni,kasa magana tayi domin ji tayi kamar an d'auke mata komai najikinta sosai jikinta ya mutu ko yatsa ta kasa d'agawa,rik'e fuskarta yayi tare da had'eta da tasa ya hura mata iska a fuska,lumshe idanuwanta tayi,muryar Musa mahaifinta taji yana cewa"ke Zarah me ki keyi a gurin nan? da sauri ta bud'e idanuwanta babu shi daga ita sai Musa, waige-waige ta kama,ya ce"ke Zahra lafiya? Bata ce komai ba ta nufi hanyar cikin gida har tana tuntu6e,shima bin bayanta yayi yana banbamin fad'a"kawa yarinya magana amma ta shareka saboda tsabar rainin wayau,duk da haka bata kulasa ba har takai d'akinsu zaunawa tayi bakin gado tare da lumshe idanuwanta tana hangenshi, "Waye shi?meye had'inta da shi? Sai yanzu zuciyarta ta fara raya mata anya mutum ne shi?,girgiza kai tayi ganin tunani bazai fishsheta ba tashi tayi ta sake alwala tanajin hayaniyar su Hanne aranta ta ce"Aikin ku kenan kullum ko gajiya bakuyi."Bayan ta idar da sallah sannan ta kwanta." Kwance take saman faffad'an k'irjinsa tana wasa da kwantaccen gashin dake k'irjin nasa mai yawa da kyau sai kwalli yake cikin murya k'asa ta ce "Honey ina sonka da yawa inason kasancewata tare da kai bana gaji da kai ko kad'an." Bai ce komai ya ci gaba da aikin da yake a computer duk da tana jikinsa amma hannunsa d'aya da computer d'ayan kuma na saman k'irjinta,tace" Ahmad a yarda nake sonka bazan iya taɓa jure inganka tare da wata ba bayan ni ina da kishi mai tsanani musamman akan ka." Murmushi kawai yayi don maganarta dariya ta basa sai ya ce"To dawa zaki ganni?" Ƙank'ameshi tayi tare da zura harshenta a kunnansa sannan a hankali ta ce"Bana tsammanin ganinka da kowa don Allah ka mini alkhawari bazaka min kishiya ba." Zuba mata ido yayi sai kuma yayi d'an murmushi yace"Hafsat me kika dafa mana yunwa nake ji." Ya fad'a domin gusar da waccen maganar,tace da sauri"am sorry honey ban d'aura ba tukun bari na tashi nayi." Ya ce"Gaskiya yunwa nake ji sosai bazan iya hak'uri har kiyi girki yanzu ba." ta ce"Ai ban ji dad'in tafiyar da Talatu mai aiki tayi ba jiya ga irinta nan,don Allah ka k'aro mana 'yan aiki." Ya ce"Karki damu yanzu shirya dai ki tashi muje gidan abinci." Zaro ido tayi ta ce"Kamarka a ganka gidan abinci ko ka mance da burin Dad akanka ne, d'aga kafad'a yayi da cewa"To idan an ganni wa yasan ni ne?sau nawa ina zuwa kuma." Murmushi tayi ta shirya da sauri, ya d'auki mota suka bar gidan sai gidan da Zahra ke aiki domin Ahmad yafi son sayen abinci ko drinks a gurin saboda suna da tsafta sosai da iya girki. [10/10, 3:51 PM] Sadfat: *SANDAR MAKAUNIYA...!* _Sabon salo._ _GAWURTATTU BIYAR._✌️ *UMMU AFFAN*🤏 🅿️ 5️⃣ & 6️⃣ Guri suka samu suka zauna, akan ɗaya daga cikin kujerun da aka ta na da domin masu sayen abinci zaunawarsu ke da wuya Zarah ta iso, hannunta d'auke da takaldar da ake mik'awa domin ka zaɓi abin da zaka saya, tun daga nesa yake kallonta cike da mamakin ganin kamar macece amma take abu na maza har ta k'araso idanuwansa na kan ta. Ɗago fuskar da zatayi ta kallesa, shi d'inma ita yake kallo zaro ido tayi tana so ta tuno inda tasan fuskar zuwa cen ta ce" *Hisham* Eh kaine *Hisham* daga Ahmad har Hafsat kallonta suke cikin k'uluwa kafin Hafsat ta ce"Ke dak'ik'iyar ina ce zaki kalli mijina ki kirasa da wani sunan daban?" Gyara tsayuwarta tayi ta ce"Mijinki? Eyhy lallai mijinki, idan har mijinki ne me yasa yake zuwar min a barcina?" Cikin maganar maza tayi maganar kamar dai yadda take yin maganarta. Cikin huci Hafsat ta ce"Ƙarya ki ke? Jahila wallahi mijina ya fi k'arfin yazo a barcinki yazo ya miki uban me? A matsayin mace ko namiji? Mata maza dake!!!" ,Zarah bata taɓa jin haushin kanta da d'abi'unta ba sai yau da matar nan ta kirata mata maza, cikin dakiyar murya da rashin tsoro ta ce"Naji ni mata maza ce ke kuwa da kika rako mata duniya fa?" A zafafe Hafsat ta d'aga hannu zata mari Zarah da sauri Aliyu ya rik'e mata hannu tare da girgiza mata kai ya ce"No Hafsat." Hawaye ne suka wanke fuskarta ta ce"Amma fa kana jin abin da ta ce? Wai kai mijina take gani a gurin bacci saboda tsabar ta raina mana wayau" ya ce"Naji to ya isa." bai sake kallon Zarah ba,ya zaunar da matarsa sannan ya kira wata a ma'aikatan gurin ya ce ga abin da suke buk'ata. Nan aka kawo musu amma Hafsat ta kasa cin komai saboda zafin da taji zuciyarta na mata,Zarah kuwa tana gurin tak'i tafiya babu abin da take sai kallon Aliyu da take kira Hisham tabbas a haka ya ma fi kyau ba kamar a baccinta ba, to amma me yasa shi bai ganeta ba bayan kuma yace yasan duk wani abu dake zuciyarta kuma ako da yaushe yana tare da ita,kallonsa kawai take,shima ta gefen ido yake lura duk da ita shi dai a zahirin gaskiya bai ta6a ganinta ba hasalima yanayin da ya ganta abin mamaki ya basa yasha ganin 'yan daudu maza dake mayar da kansu mata amma bai ta6a ganin macen dake mayar da kanta namiji ba sai a kanta." Ganin Hafsat tak'i cin komai yasa dole ya ce amata take away,bayan ya biya komai suka fita,Zarah bin bayansu tayi tana ganin sun shiga mota hau acha6a tace duk inda sukayi ya bisu,Aliyu ya lura da ita sosai yayi mamakinta to me take nufi?,ya tambayi kansa bashi da amsa,kai tsaye gidansa ya nufa bayan yayi hune mai gadi ya bud'e masa ya shiga,Zarah sauka tayi daga babyur bayan ta biyasa ya wuce,kai tsaye gate d'in ta nufa ta fara bubbugawa,Mai gadi ya lek'o,kallonta yayi sama da k'asa yace"lafiya?cikin maganar tata tace"haba Baaba ka bani guri na wuce gurin Hisham nazo,kallonta yayi tare da d'aure fuska yace"wuce ki bamu guri 'yar dauduwa nan ba gidan sakarai bane." Matsowa tayi kusa dashi tare da chafkar wuyansa ta shak'e sosai yaji tsoro domin itan kanta Zarah bata san tana da k'arfin hakan ba tasan dai duk abinda yazo zuciyarta tana ai watar dashi ne tace"zaka bud'emin ko sai kajika barzahu?,da sauri ya gyad'a kai,dai-dai fitowar Aliyu da sauri ya k'araso tare da bige hannunta a wuyan mai gadi da sauri ta sakesa,cikin fushi yace"wai meye damuwarki da ni ne?me ya kawoki gidana?,matsowa tayi kusa dashi da sarauni kuma ta matsa abinda wani mutum bai ta6a mata ba shine Aliyu ya mata wato kwarjini sai ta kasa magana,yace"maza kija k'afarki ki barmin gida kafin nasa securitys su fitar min dake,sosa kai tayi sannan tace"amma Hisham ka bani mamaki da ka kasa gane ni amma yanzu zan tafi kamar yadda ka buk'ata sai dai ka sani zan dawo,cilla k'afa ta bara tare da bonsewa ta fara tafiya,daga Aliyu har mai gadi baki bud'e suke kallonta,kafin yaja tsaki ya koma ciki shima mai gadi yabi bayansa da sauri don ji yayi kamar zata(Matsoraci🤪). ........................... Da sallama ya shugo cikin katafaran parloun da ya tsaru iya tsaruwa an kashe mak'udan kud'i wajen tsarashi da kayan alatu na zamani,wata Hajiya ce wacce bazata haura shekaru 45y ba zaune kan d'aya daga kujerun alfarma dake parloun,ko da ya shugo baibi takanta ba da sauri ya nufi cikin wani kad'i wanda shi kad'ai ke shiga d'akin sai kuwa Alhaji Mudi amininsa,binsa tayi da kallo lokaci guda wasu hawaye masu zafi suka zubo mata Hajiya Falmata kenan mata a gurin Alhaji Kabiru Tafida mai neman takarar kujerar gwamna,jagwab ta koma ta zauna hawayen basu dena zuba a fuskarta ba,yaushe xata dena kuka?yaushe hawayenta zasu tsaya?har abada zuciyarta ta bata amsa,sosai ta fashe da kuka tare da d'aga hannuwanta sama tace"Allah gani gareka kasan irin halin da nake ciki Allah ka kawo min a gaji cikin gaggawa." Ta fashe da kuka sosai,shi kuwa Alhaji Tafida yana shiga d'akinsa dake dund'un ya fara wata magana ta sulkulle kafin wani haske ya bayyana,ai abubuwan da na gani sauran kad'an birona ya fad'i domin fitsari naji ya fara zubomin lolx,Wani mutum na gani zurdur haihuwar uwarsa a tsaye kansa an masa aski yayin da duk jikinsa wasu irin zanene a cikinsa da ja da bak'i idanuwansa duka a bud'e yayin da hancinsa ke fitar da wani hayak'i haka bakinsa a bud'e yake sosai,gefe guda kawunan mutane ne a k'asa harda gangar jikin wasu ga dai abubuwa nan babu kyawun gani,daga k'asan mutumin wani bakin mutum ne bak'i sosai kaine kawai ba jiki shine ya fara magana cikon wani irin yanayi,murya mara dad'in sauraro da alamar shine dodon nasa yace"Tafida baza ka ta6a mulki ba idan har baka bamu jinin wanda muka buk'ata ba jininsa kawai ne zaiyi tasiri da samun kwarjininka a gurin jama'a har su za6eka,jikin Alhaji Tafida har rawa yake yace"Dodo nayi alkhawarin baka ko ma jinin waye tunda na baka mahaifiyata na baka wasu daga jinina waye ma bazan iya baka ba,ni jinin sarauta ne bana buk'atar sarauta sai mulki irin na siyasa nayi alkhawarin baka koma menene matuk'ar zanyi kud'i zanyi mulki." Hhhhhhhhhh hhhhhhhhhhh hhhhhhhhhh dodon nan yake dariya kafin yace"Alhaji Mahmud!! Mahmuda!!! Mahmuda!!! Mai Abaya!!!!!,duk da jikin Alhaji Kabiru Tafida yayi sanyi da jin abinda dodonsa ya kira amma haka ya k'arasa jikin wannan mutumin dake zindur ya bigi kansa da k'arfi yanayin wasu surutai sai kud'i suka dunga 6ul6ulowa ta cikin bakinsa,saida ya jika jaka guda sannan ya d'auki wata kwalya da ta bayyana jini ne a ciki sha yayi sannan ya kinkimi jakar ya fita." Har lokacin tana parloun tana hawaye ya fito,wani kallo ya mata ya nufi hanyar fita,cikin kuka tace"Duk abinda kake shukawa k'arshenka na nan zuwa,Allah ba azzalimin bawa bane Alhaji Tafida Allah ya tona maka asiri!!!,ta idasa cikin k'ara da kuka,juyowa yayi tare da sakin wata dariya "Hahhahhhahhhahhhhahhh!! Falmata har abada inaso ki sani asirina bazai ta6a tonuwa ba yana nan a rufe har k'asa ta tashi,cikin kuka tace"mulki da siyasa ne burinka kuma har abada bazaka samu ba kasa wannan a zuciyarka mugu azzalumi,K'arasowa yayi ya sakar mata wani wawan mari kuka ta saka da k'arfi tare da zubewa gurin tana kuka kamar ranta zai fita,k'afa yasa ya fita cikin gidan,yana fitowa ya saka key ya rufe ko ina na ciki,abun ya bani matuk'ar mamaki da naga wannan yanken shine k'arami a cikin part-part dake gidan kuma shine a baya cen k'arshen gidan da alama babu wanda ke zuwa gurin domin sai anyi tafiya mai tsawo sannan za'a kai wajen shi kansa a mota yazo,bud'e bayan motar yayi tare da chilla jakar ciki sannan ya shiga ya tana motar,babban part d'in da yafi ko wanne girma a ciki naga tsaya domin rassa ne har guda biyar a gidan gida ne na family yana parking ya fito tare da shiga ciki nan had'imai suka fara gaishesa ko kallonsu bai yiba bare su saka ran zai amsa gaisuwarsu,sama ya nufa Hajiya Balaraba zaune hamshak'e cikin shiga ta alfarma ga zinarai da gwala-gwalai a wuyanta sai shek'i suke,yana shugowa ta dubesa da murmushi zaunawa yayi yana maida numfashi tace"lafiya na ganka cikin damuwa Alhaji?yace"uhmmm Hajiya kedai bari kawai,mik'ewa yayi zai shiga ciki tace"amma kuma Saif ya kirani da ba kanan,Cheek ya tsaya tare da komawa ya zauna yace"meke damunsa?tace"maganar gizo bata wuce ta k'ok'i maganar kud'i ce,yace"to meye amfaninsu tunda ina dasu ai amfaninsu kenan bawa d'ana duk abinda yake so,waya ya ciro tare da kiran wayar Saif wanda yake k'asar Englang yana karatunsa ko ince shak'iyanci a gurinsu yana karatu ne amma babu abinda yake sai shagalinsa da matan turawa manemin mata ne na k'arshe da shaye-shaye d'an hutu ne mahaifinsa na k'aunarsa fiye da zaton mai karatu zai iya yin komai akan soyayyar d'ansa komai yake so bai rasaba babu abinda ya nema ya samu yana d'aya daga cikin abinda ya lalatashi shida k'anwarsa Raihanatu da suke kira Rihah dukansu a k'asar waje suke karatu mahaifinsu ya killacesu baya son komai ya samesu hakan yasa tun daga secondry a waje suke karatu har zuwa yanzu da Saif ke karatun masters d'insa ita kuma Riha a SS2 take hutu kawai ke dawo da Rihah gida shi kuwa Saif sai yaso yake dawowa domin sosai ya tsani Nigeria,Saif ne ya d'aga kiran mahaifinsa wanda a lokacin rungume yake da wata cika dukansu tsirara yace"My Dad ya kake?,yace"ina lafiya my son ya karatun?"Alhamdulillah,ya basa amsa sannan ya d'aura da cewa"Dad Mum ta sanar da kai buk'atata,yace"yes yanzu zan maka transfer ta account d'inka karka damu danku nake neman kud'in nan idan har kai da 'yar uwarka da mahaifiyarku za kuji dad'i to kowama kar yaji,yace"wow Dad shi yasa nake sonka."duka suka saki dariya yace"Dad yanzu zan shiga lucture zan kiraka anjima ka turon kud'in yanzu,yace"ok my son kayi karatu da yawa,da haka ya yenke kiran,Hajiya Balaraba tabi mijin nata da kallo cikin sakin murmushi naji dad'i tana son yarda yake nuna tsantsar k'auna a garesu,tashi yayi ya wuce sama yana danna kiran Alhaji Mudi bayan ya d'auka yace"Naje d'akin dodo na d'auko kud'in ina son ka turo a amsar maka da kud'in nan a sayo makamai da bindigogi da kayan maye wad'anda za'a bawa yaran nan 'yan bangar siyasa,Alhaji Mudi yace"ok hakan yayi sannan ya yanke kiran turawa Saif dubu d'ari uku yayi sannan ya kwanta cike da tunanin hanyar da zasuci gaba dayi domin ganin sun sami mulkin nan ta halin k'ak'a da ganin yarda zasu dakatar da Alhaji Mahmud Mai Abaya gwamnatin dake ci yanzu." ................................. Ko da Zarah ta koma wajen aikinta cike take da mamakin dalilin da zaisa Hisham ya mata haka,sai yanzu zuciyarta ta bata"Zarah wancen fa mafarki ne wannan kuma zahiri,uhmmm taja numfashi da haka har na kammala aikinta ta dawo gida wanka tayi tare da d'aura alwala kamar kullum,Musa ya shugo cikin gidan yana k'wala mata kira,"Zahra'u"Zahra'u,ta shi tayi tana niyyar fitowa sai gashi ya shugo sai ta komo ciki ta sami guri ta zauna kallonta yayi da cewa"Zarah wata gasa zamu shiga akan chacha duk wanda yaci a cikinmu shi keda dukiya kinga dole sai kowa ya bada kudi shine akace ni na mata dubu d'ari shi kuma abokin takarar tawa zaibada dubu dari biyar kinaji ko idan ni nace zan had'e duka na rik'e haka idan shi amma yarda nake da sa'a ban ta6a chacha aka cini ba don haka wannan ma bana ganin za'a cini,cikin maganarta ta kwalawa tace"yo toni ina ruwana a harkarka da zakazo min da wannan maganar,gwara murya yayi da samun guri ya zauna cikin sanyin murya yace"Zarah akwai ruwanki kinga ke kina aiki kuma zuwa yanzu nasan kin tara kudi fiye da dubu d'ari shine nakeso ki rantamin idan munyi zan baki d'ari biyu kinga na nunka miki,wani kallo ta masa tare da mik'ewa tace"amma fa kai Musan nan ka iya rainin hankali nice zan baka aron kud'i?,yace"eh mana Zarah nace miki zan nunka miki ne idan naci,tace"to idan bakaci ba fa?,yace"haba Zarah ya zakimin wannan fatan zan ma ci,tace"to ko ina dasu bazan baka ba bare ma banda su,k'ara sanyin murya yayi yace"haba Zarah kiyi hakuri ki aramin,d'aga murya tayi"yasin ka fitar min d'aki kafin na kira maka 'yan sanda ince zaka min sata,Feesu ce ta shugo wani kallo banza ta masa tace"Musa mai ka shugo ka mana a d'aki?,yace"wallahi duk na haifi 'yan iskan 'ya'ya wai bani ne ubanku ba da kuke kiran sunana kai tsaye?,Feesu tasa dariya tace"kaine amma kaida kanka ka koya mana kiranka da Musa ita kuma matar da Hanne don haka baku koyar damu kiran Baba da Mama ba da zamu kiraku da hakan,Zarah tace"ai kuwa don kuwa barewa bazati gudu d'anta yayi rarrafe ba,fita yayi yana mitar tau dai mun aifi bala'i,Feesu tace"kaine zaka gansa bala'in." Zarah shinfind'a dadduma tayi ta fara sallah,fisu handbag d'inta ta d'auka ta fice,Yau indomie taci da ta dafa yanzu da kwai sannan ta d'an dad'e a zaune ta kwanta,Kamar kullum yauma sai ganinsa tayi ya bayyanar mata. [10/10, 3:56 PM] Sadfat: *SANDAR MAKAUNIYA...!* _GAWURTATTU BIYAR TAKU NA✌️._ *UMMU AFFAN*🤏 🅿️ 7️⃣ & 8️⃣ ..."Hisham!!!" Ta kira sunanshi cikin sauti, murmushi d'auke a fuskarsa ya ƙara so ya ce, "Eh ni ne" Girgiza kai ta fara da fad'in "A'a!a'a!!a'a!!!!!" Sai ta farko a matuk'ar gigice waige-waige ta fara. Duhun dare ya tsala sosai gata ita d'aya a d'akin kamar mayya, bata taɓa jin zuciyarta ta karaya ba irin na yau. Hawaye take ita da abu da yawa bai sata kuka kai ita fa duk tausayin da abu ya bata da wuya tayi kuka amma yau ita ke kuka, ganinsa tayi tsaye gabanta, baya ta fara tana girgiza kai, shima k'ara kusanto ta yake sai da yazo daf da ita sannan ya sami guri ya zauna kama hannuwanta ya yi ya ce, "Ki dena kuka masoyiyata wani ma bana so ya saki kuka balle ni, kukanki na d'aya daga cikin abin da zai tayar min da hankali zan iya jure komai amma ban iya jure ganinki cikin damuwa da tashin hankali." Cikin kuka ta ce"Ni ka rabu dani bana sonka ba na son ganinka!!" Da k'arfi ya rumtse idanuwansa sannan ya bud'e ita kan ta sai da ya bata tsoro ganin yarda lokaci guda idanuwan nasa suka chenja kala, juyewa da farare zuwa baƙaƙe ba ma ja ba, abin da furgitarwa, ya ce"ban ce lallai ki soni ba amma ni ki sani ina sonki! ina sonki!! ina sonki!!! da k'arfi ya jawota jikinsa tare da had'e bakinsu guri guda,turesa take amma jinsa take kamar tana ture k'arfe ko wani gumgume man dutse,sai da ya gaji don kansa sannan ya saketa amma har lokacin bai bari tabar jikinsa ba,ya ce"na ta'ba fad'a miki ako da yaushe ina tare da ke babu wanda ya isa ya rabamu dake,ta ce"jiya na ganka da matarka ai" Zaro ido yayi sosai sai kuma yayi shuru ta ce"eh na ganka naji ta kira ka da mijinta kuma kun hau mota kun je gida mai yasa a lokacin da na maka magana baka kulani ba kace baka sanni ba!?" Girgiza kai yayi da sauri yace"Ba ni bane, ni Hisham sunana!" ,ta ce"k'arya kake kaine na gani,ya ce"bani bane wancen bil a........sai kuma yayi shuru ya ce"bani bane!bani bane!!! 'bat ya 'bace sama ko k'asa a furgice ta farka duk ta had'a zufa,ashe wacce farkawar ta farko duk a cikin mafarkin tayi ta,kurma ihuww tayi da k'arfi sai ga Hanne ta shugo"ke lafiya?ta tambayeta sai a lokacin ta bud'e ido,Hanne ta ce"kusan kullum ke haka kike barcinki me ke faruwa dake ne?" girgiza kai ta fara ta ce"ba komai" zaunawa Hanne tayi tare da dafa kafad'ar Zarah ta ce"ki sanar dani abin da ke damunki Zarah?" girgiza kai tayi"ba komai,ganin Hanne na niyyar takura mata sai ta tashi ta bata guri wanka taje tayi wajen tara na safe sai lokacin take sallah,bayan ta idar ta dad'e zaune tana tunani amma zuciyarta ta kasa tunano mata komai,tashi tayi ta shirya zuwa wajen aiki ko karyawa bata iya yiba,tana fitowa taga 'yan makarantar islamiyya suna wucewa kasancewar ranar Asabar ce,gabanta taji ya fad'i tabi su da kallo har suka 'bace sannan taci gaba da tafiya.Ta wajen da su Musa ke chacha ta wuce,ko kallonsu batayi ba bare ta gaishe su,wani cikin mazauna gurin yana hura sigari yace"Musa waccen ba Zarah bace ta wuce?Da sauri ya d'ago kansa yace"ita ce mana ina ruwanka da ita?yace"daman ni bance wani abuba ko gurinta kaga naje kawai dai kai dai yaranka basu da tarbiyya da d'a'a ace suka abokan ubansu amma suk'i gaishe su,yace"ai kai naka yaran naga tarbiyyar gare su,nan fa abu kamar wasa ya kaisu ga chachar baki harda k'ok'arin dambe da k'yar aka rabasu." .............................. Hafsat ce kwance a saman k'irjin mijinta a hankali yake shafa bayanta,ya ce"gobe ne Alhaji ya sanar dani zamuje Bakori yak'in neman za'be akwai wani babban taro da za'ayi a cen,k'ara shigewa k'irjinsa tayi tace"bana so kana nisa dani Honey,a hankali ya kai hannu saman cikinta yace"yaushe zaki haifa mana baby?,zaro ido tayi tace"baby kuma?tun yanzun?cike da mamaki ya kalleta yace"to idan ba yanzu ba sai yaushe?,murmushi ta sakar masa tace"kana son na haihu Ahmad?,ya ce"kin san ina son yara ko?,har yanzu murmushi take ta ce"shi kenan a yau ka bani yaro,d'an murmushi yayi ya ce"kice dai Allah ya bamu,a zuciyarta ta ce"ba amin ba,a fili kuwa murmushi tayi,babu a binda ta tsana a yanzu irin haihuwa duk da kimanin shekaru biyu kenan da auransu,tunda akayi auransu ta fara planning don sau biyu kenan tanayi na shekara-shekara take allura da farko tayi ana gobe bikinsu sannan kuma data shekara ta koma yanzu haka ta kusan komawa tayi wata Allah ya gani yarda take son mijinta da son more rayuwa bata jin zata haihu anan kusa domin gani take da ta haihu shikenan Ahmad zai juya mata baya ita kuma ta tsofe,shiyasa bata shiryawa haihuwa nan kusa ba,duk wata hanya da tasan zai gane ta tosheta shiyasa ma tafi yarda da allura akan kwaya." Ta'bata da yayi ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta afka,Sajensa ta fara shafawa a hankali,ya ce"tunanin me kike?tace"haihuwa Ahmad haihuwa ta Allah ce don Allah kar kaga ban haihu ba ka juya min baya ko kace zaka min kishiya." Jawota yayi jikinsa yana shafa bayanta yace"karki damu Hafsat ni ba wai na damu bane duka yaushe mukayi auran da har zan d'aga hankalina kawai dai na fad'a miki ina son yara ne sai ki shirya haifa min kyawawan yara kamarki,cikin shagwa'ba ta ce"kamarka dai ni har wani kyau gare ni da za'ace kamata,ni nafi son kyakkyawan yaro kamarka,ya ce"shi kenan sai muyi anko da masu kama dake da masu kama dani,murmushi kawai tayi tare da k'ara shegewa jikinsa." *BAKORI k'aramar hukumar jahar Katsina* Sosai mutane suka cika,inda ake ta d'agawa gwamna Alhaji Mahmud mai abaya hannu *Ahmad Mahmud mai abaya* shine saman mumbari yana bayanin manufofinsu kamar yadda mahaifinsa ya basa dama,cikin k'wararran turancinsa yake magana ya ce" wannan gwamnati dai ita ce akan mulki sannan ko talakawa kun fi mu sanin meye manufarmu domin kuna gani a k'asa aiyukanyi matasanmu sun sama domin gina masana'antu da gwamnatin nan tamu tayi fannin noma muna bakin k'ok'ari domin ganin mun bawa manobanmu tallafi domin noman zamani ba wannan ba duba da yarda muka gina makarantu da kasuwanni domin ci gaban da samar da ilmi a jaharmu,muna kira gareku daku k'ara bamu k'uruk'unku domin mu idasa aiyukan da muka faro.ihuww da tafi aka saka mai abaya babu abinda yake sai murmushi ta k'ara jin alfahari da d'an nasa,wanda ya amshi abun magana ne bayan Aliyu ya koma ya zauna yace"ANPC jama'a suka amshe da NASARA SA'A *ANPC* suka sake cewa NASARA SA'A CHENJI, *ANPC* nasara sannan yaci gaba da bayaninsa duk akan aiyukan da suke da son samun k'uruk'un jama'a." ........................... Alhaji Tafida ne zaune da amininsa Alhaji Mudi,akan kujeru ga taron matasa gabansu da kayan sara suka su adduna wuk'ak'e bindiga da sauransu sai gayan maye taba wiwi shalaso da hudar iblis. Ogansu wato Habu shine ya tashi ya fara rabawa kowa nashi,sosai sukasha kayan mayen a gabansu Alhaji Tafida ba 'abin da suke sai hirarsu sun tara yaran talakawa suna basu kayan maye da adduna nasu kuwa sun killace su sun fitar dasu k'asar ma ko kud'a masa burin ya ta'basu,bayan sun gama sannan suka d'unguma dukansu domin zuwa yak'in neman za'be,sosai suma suka tara jama'a ba abinda suke sai rabon kud'i damansu nasu na rabon kud'i komai suna yinsa cikin nera"PRP jam'iyyar hamayya kenan ko ina photunan Alhaji Tafida ne ana faman bi ana lik'a fad'i suke"Sai kayi gwamna sai kayi,ba abinda ya ke saki sai murmushi yana d'agawa jama'a hannu da d'aukar musu alkhawarin idan suka za'besa zai musu aiki mai nagarta wanda gwamnatin dake kai takasayi inda suke sukar gwamnati maici yanzu da cewa idan har suka bari wannan gwamnati ta maimaita to sai dai azo ana d'aukar talakawa matattu a gidajensu domin yunwa da rashin arzik'i da abinci da ake fama dashi yace"meye a cikin wannan gwamnatin bayan son kansu da 'ya'yansu ba sama talakawan da suka za'besu komai ba gyara harkar ilmi ta lalace idan har kuka za'be mu 'ya'yanku zasuyi karatu kyauta harkar noma zata bunk'asa zamu gina muku makarantu da masana'antu kowa zaiji dad'i shine fatanmu,tafi aka fara rab-rab-rab da ihuww murmushi kawai yake saki,fatansa da hangensa ganin ya tsallake wannan za'ben dake tunkarowa." "Ni kan Zarah yau lafiyarki k'alau kuwa? cewar Abida wacce suke aiki tare idan ma bazata wuce sa'ar Zarah ba suna gaisawa sosai don zan iya cewa a gurin tafi shiri da Abida saboda yarinya ce mai natsuwa,gyara tsayuwarta tayi tace"a kwai wani abu da na manta da ya faru dani a rayuwata amma sam na kasa tunawa,murmushi Abida tayi tace"to ke dole sai kin tuna kawai ki bar komai karki takurawa k'wak'walwarki idan lokacin ki sanin yayi zaki sani." Dariya Zarah tayi tace"dad'ina da ke kanki naja 'yan mata." kama hannunta tayi suka fara aiki, Abida tace"amma Zarah na tambayeki badamuwa?,Zarah na gyara kwalar rigarta tace"ina jinki,d'an shuru tayi sai kuma tace"am me yasa kike saka kayan maza?me yasa kije magana irin ta maza?,da sauri Zarah ta kalleta sai kuma tayi murmushi tana buga bayanta tace"karki damu da wannan,ta fad'a har ila yau cikin maganarta ta d'aura da cewa"kawai ki share,haka sukaci gaba da aikinsu k'arfe uku da rabi Abida ta musu sallama domin lokacin ita take tafiya Zarah tace"amma me yasa kike tafiya tun yanzu?,tace"eh saboda islamiyya nake zuwa da k'anne na k'arfe hud'u zanje na shiryasu nima na shirya sai muwuce,gyad'a kai kawai Zarah tayi tabita da kallo sannan ta koma ciki." .................. "Hafsat"Hafsat"Hafsat ki tashi lafiya?wai meke faruwa ne? kusa da ita ya zauna tare da d'agota jikinsa,sai kawai yaga ta bud'e ido tana dariya,ajiyar zuciya ya saki tare da cewa"wannan wane irin wasa ne please ki dena,hannunta tasa ta sak'alo wuyansa tare da had'e bakinsu guri guda tana tsotsa,zuwa cen ta saki ta kuma sake mayarwa tana tsotsa a hankali ta saki bakinsa idanuwanta akan la'b'bansa tace"ban gaji bane." da me? ya tambayeta tace"kafini sani ai "ta fad'a tana sake jawosa jikinta,murmushi kawai yayi aransa yana mamakin jaraba irin ta Hafsat,yace"ki shirya yau zamuje gida,tace"bayan mun gama ko? harararta yayi ta saki dariya nan suka fad'a saman bed." Sun sami Mai abaya da bak'i hakan yasa kai tsaye suka wuce cikin gidan gwamnatin,Ita kanta Hajiya Batula cikin shiri take domin zasu fita wajen k'addamar da wata k'ungiya ta mata sai Hajiya Anty don a tsaitsaye suka gaisa ta fita,sai gurin Hajiya Anty ta tauza suka d'an ta'ba hira shi kuwa Ahmad tuni ya fita wajen Daddynsa." .................. "Wai ke Rihah ko d'anya kuka sami hutu sai kin taho,amma nace miki hutun da baifi sati biyu ba ki dunga zamanki cen meye amfanin gidan da na saya muku keda yayanki Saif,hawaye ne kwance a idaniyarta amma bata bari sun zubo ba tayi k'ok'arin mayar da su tace''kayi hak'uri Daddy laifi ne don 'ya taso ganin iyayenta?,yace"ba laifi bane Rihah amma ina son inga kunyi ingantaccen ilmi da babu kamarsa ina son naga kunfi kowa,tace"na sani Daddy kayi hakuri,ransa 'ba ce yabar gurin,hawayen da take 'boyewa suka zubo jiki a sanyaye ta koma kusa da Ummanta tare da d'aura kanta akan kafad'arta Umman tace"Rihah Abbanku yafi son ganinku acen kuna karatunku ke kuma kina son zuwa gida me yasa? cikin kuka tace"shikenan mu kuma acen zamu k'are bazamu dawo k'asarmu kusa da danginmu da iyayenmu ba Umma kinsan bani da ra'ayin karatun waje Abba ne ya takuramin gashinan silar haka ya jefa rayuwar Yah Saif cikin wani mummunan ha....Umma ta katseta ta hanyar d'aga mata hannu tace"kinga kad'an daga cikin halayenki ko?yanzu Yayan naki kike son jawa wani mugun alkaba'in?yaro yana cen ya mayar da hankali ga karatunsa ba irinki ba,sosai Rihah ke hawaye tana girgiza kai zatayi magana Umma ta d'aga mata hannu"Raihanatu bana son kiyi wata magana anan bazaki jawa yarona wani abunba waike mai yasa baki fad'an alkhairi ne." tana kaiwa nan ta wuce tana mita." Riha zamewa a gurin tayi tana hawaye cike da takaici hali irin na iyayenta,sosai take kuka aranta tanaji ina ma basu suka haifeta ba,tashi tayi ta fito,chekk ta tsaya ta zubawa part d'in da take tsaye gurin ido sosai hawaye suka fara zubo mata kamar kullum ko da yaushe idan tazo k'asar sai ta shiga ciki duk da a yanzu babu kowa a ciki,sai dai komai nasu yana nan tsaf yarda yake domin Kakansu yana sawa a gyara part d'in duk bayan sati guda,kai tsaye d'akin 'yar uwarta aminiyarta k'awarta masoyiyarta ta shiga,zaunawa tayi bakin tangameman gadonta tana kuka tace a fili "Abbu Ammi da aminiyata ta fad'a cikin kuka mai tsuma zuciya,wani pic dake saman gadon ta d'auka,Abbu da Ammi sai wata matashiyar budurwa a tsakiyarsu duka sun rik'eta cikin murmushi sosai sukayi kyau,rungume pic d'in tayi tana kuka,ta kusan awa biyu a bedroom d'in sannan ta sake gyara d'akin tafito tana waiwaye da hawaye a idonta,part d'in Kakansu ta wuce tsoho mai ran k'arfe hakimin Katsina duk da yanzu ya tsufa d'ansa na biyu ne ya gajesa mai biwa Alhaji Tafida dominshi Abban su Rihan yace"sarauta bata gabansa siyasa ce gabansa,da sallama ta shiga ciki da fara'a ta nufi tsohon wanda ta iske zaune a parliunsa sai hadimansa dake masa komai cikin fara'a yace"wacece na ke gani kama RAIHANATU tsohuwar matar hakimi,sosai ta saka daruya da k'arawa gabansa tana son tsohon nan sosai cikin shagwa'ba ta ce..... [10/10, 4:01 PM] Sadfat: *SANDAR MAKAUNIYA...!* _Sabon salo._ _GAWURTATTU BIYAR TAKU NA✌️._ *UMMU AFFAN*🤏 🅿️ 9️⃣ & 🔟 Ta ce, "Ni ba tsohuwa ba ce kaine tsoho" "Kina gani na yaro sabon jini ki kirani wani tsoho? To ke kan ki kin mini tsofa." Gaba d'aya suka saka dariya, zaunawa tayi ta ce, "Kaka ina wuni'' ya ce"Lafiya k'alau ya karatun naku" "AlhamduLillah Kaka." Zaunawa tayi sukayi hira sosai domin haka yake mutum ne mai sakin jiki da son jikokinsa." Kusan awarta biyu a gurin tsohon suna hira, yana son Rihah a cikin jikokinsa saboda kyawun halinta yarinya ce k'ara amma tana da k'wak'walwar manya, jin kiran sallah ya tasar da ita ta ma shi sallama sannan ta wuce part d'insu. Sallah tayi sannan ta sake fitowa ta nufi sauran sassan gidan k'annan mahaifinta su biyu Alhaji Kamalu wanda shine MAGAJIN GARIN Katsina sai Alhaji Auwalu, dukansu suna da mata da yara kuma duk anan gidan suke da zama kowa da part d'insa. Tafiya take tana tunanin rayuwa da abin da ya faru baya duk da lokacin ba wani wayau ne da ita ba amma tana tuna wasu abubuwan, tsayawa tayi cheek lokacin da idanuwanta suka kai ga wannan ginin na cen k'arshen gidansu k'urawa gurin ido tayi zuciyarta cike da zullumi tun da ta taso take ganin wancen ginin ada dai tasan na hadiman gidan ne amma a yanzu Abbanta tuntuni ya kulle gurin kuma babu me shiga dagashi sai amininsa abun na damunta sosai tana son sanin me suke shiga yi domin ita kad'ai ce bata yarda da shi ba, shi kan shi Abban ya sani don dodonsa ya sanar masa komai dalilin da yasa bai son zamanta k'asar kenan, ta ra sa dalilin da yasa sam k'annan mahaifinta basa magana akan hakan duk da tana ganin take-taken Abban nasu kamar yayi wani abun a kan hakan, a hankali ta fara takawa k'irjinta na bugawa sosai, tana tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki,da haka har ta kusan k'arasawa,Mahaifinta ne ta ga ya fito daga ciki,da sauri ta juya tayi kamar ba gurin take nufa ba,ya ganta amma bai ce mata komai ba,da haka ta samu ta k'arasa part d'insu tana shiga kai tsaye bedroom d'inta ta wuce ta fad'a saman bed tare da sakin wani irin kuka mai tsuma zuciya ta nad'e guri guda ta cure tana kuka sosai jin muryar mahaifinta yasa ta tsayar da kukanta chek"Riha "Riha "Riha kina ina ne?" Jikinta har rawa yake ta fito kan ta a k'asa bata yarda ta d'ago kai ta dubeshi ba,cikin tsananin masifa ya ce"Raihanatu ki kiyayeni ki fita sabgata idan ba so kike kema ki shiga cikin taskona ba,ina mai umartarki ko hanyar da zaki BQ kika sake bi wallahi ranki sai ya 'baci zan iya sallamaki wallahi idan har naga zaki kawo min matsala." Hawaye ne ke bin kuncinta cikin sanyin murya ta ce"To Abba." Mtsuuw!yaja tsaki tare da barin gurin yana mita,a gurin ta zube tana kuka sosai Umma ta fito ta ce"Ke dai wannan yarinyar ban san halin wacce kika gado ba,ni dai ba haka nake ba ubanki ma mai zafi ne sai dai a cikin danginsa kikayo gado ni dai ba haka nawa dangin suke ba." Tana gama fad'a tabar gurin Riha ta sake sakin kuka cike da tausayin kanta da na familynsu. ********* "Zarah! Zarah!!" Habu ne ya shugo yana k'wala mata kira,fitowa tayi daga d'aki fuskar nan tata a d'aure,ta ce"kai Habu lafiya kake min irin wannan kiran kamar kana bina bashi,ya ce"ke dalla karki raina min wayau ta samu ne idan zaki iya? Su Alhaji Tafida ke son 'yan mata za su musu wani aiki shine nace zan nemoki" Wani kallo ta mashi da Ƙwalawa da rainin hankali ta ce"Waye hakan?" ya ce"Ubangidanmu ne shi nakewa aiki yana neman gwamnan jaha ne, amma kuma ma na tuna ba ke ya kamata na saba Feesu zatafi iyawa ke kina abu kamar maza ma taya zaki iya." Mtsuuww taja tsaki ta ce"Kuje kuyi ta musu aiki kuna shan bak'ar wahala sun raina yaran talakawa nasu yaran sun killace su,ku ne da musu bauta idan sunci su manta daku dagasu sai matayensu da yaransu kune shashashai suna amfani daku suna baku kayan maye da makamai wallahi Habu kayi hankali 'yan siyasar nan ba k'aunace suke nuna muku ba!" ,ya ce"dalla rufemin baki ke ina ruwanki tun da bazakiyi ba kinji nace miki dole?" Yayi ficewarshi yana tan gad'i. tsaki taja tare da shiga d'akin Hanne. Hanne da ke d'aura kulle-kullenta da take sayarwa,su kuka,ku'bewa busassa,su gishiri,da maggi d'an kulli,ta d'ago tana kallo Zarah,wacce ta sami guri ta zauna bakin tsohon gadonta. Hanne ta ce"yanzu na gama gyara gadon sai kizo ki zauna ki 'bata min saboda ga marainiyar wayonki?" Zarah ta kad'a kai ta ce"ko mai zaki ce sai dai ki ce, ni nazo in tambayeki ne, gyara zama tayi tana gallawa Zarah harara ta ce"Ina jinki don idan ma kud'i ne wallahi kar ki soma tambayata don ban da su, ke ko ina dasu bazan baki ba." ta ce"ni nace miki kud'inki na ke so?me kike dashi da zaki bani Hanne?,tsuke baki tayi kafin a hankali ta ce"naji bani da shin kiyi tambayarki ki tashi ki bar min d'aki." Zarah ta ce"daman tambayarki zanyi mai yasa baku bamu tarbiyya ba?me yasa ku ba iyaye bane kamar sauran wasu iyayen." Kama ha'ba Hanne tayi da zaro ido ta ce"oh! kinzo ki tuhume ni ne?to ban sani ba,kuma ki tashi ki bar min d'aki." Mik'ewa Zarah tayi ta ce"ko ba kice in fita ba daman fita zanyi ni wallahi ji nake ina ma baku ne iyayena ba." Sosai Hanne ta zaro ido tare da mik'ewa tsaye ta zuba ma Zarah ido wacce ke yarfe hannu da ciccijewa wai irin bonsewar nan,Hanne ta ce"to don ubanki ki canja iyayen mana." Zarah ta ce"da a kwai halin haka da nayi" tana fad'a ta fice." Tsuww!!! Hanne taja tsaki taci gaba da aikinta tana mita,Zarah d'akinsu ta wuce tayi shirinta domin fita gurin aiki a ranta tana mai jin haushin iyayen nata,babban abun takaici tana fita taga an kawo Musa jane-jane da jini wai sunyi fad'a garin gaddamar cha-cha,kamar ta wuce amma ganin halin da yake yasa ta tsaya ita ba tausayinsa taji ba domin sam bata da tausayi idan akan k'arya ne,wani a ciki ya ce"yauwa Zarah gara da kika fito gashi nan ku kaishi asibiti idan ba haka ba kuwa akwai matsala." Wani hura hanci tayi ganin sun jibgeshi gabanta kuma sun wuce. Ciki ta shiga tare da kiran Hanne wacce tana ganinsa ta rud'e ta fara kururuwa bayan da zai fita da fad'a suka rabu (Allah sarki akace tsakanin mata da miji sai Allah),harara Zarah kawai take aika mata kafin ta ce"to ke ya za'ayi yanzu?kin tsaya kinawa mutane kuka." Habu ne ya iso gurin kallonsu yayi yana rangaji "me ke faruwa ne?" ya fad'a cikin muryarsu ta mashaya da daba,Hanne cikin kuka ta ce"Habu ina zan sani ni dai gani nayi Zarah ta kirani na gansa anan" Kallon Zarah yayi ya ce"ke kuma ya akayi ne kin zuba min ido sai kace na mujiya.'" harararshi tayi dacewa"Ai gara nawa akan naka ni dai nasan na gaba yayi gaba, na baya sai labari." ya ce"to naji me ya sami wannan mutumin?" Ya fad'a yana nuna Musa wai mahaifinsa ne mutumin. ta ce"su Saminu ne abokinsa suka kawosa wai sunyi fad'a akan gardamar chacha kuma idan ba'a kai shi asibiti ba da matsala." aljihu yasa hannu sai gashi ya fito da dubu biyar ya ce"yaci sa'a yasin daga gidan Alajina nake na sami kud'i da sai dai ya mutu a haka" Hanne ya ba mawa ya ce"ku kaishi asibiti,Sannan ya shige cikin gida kamar zai kifa. Zarah ta kira mai napep sannan ya taimaka musu suka shigar dashi ciki sannan suka wuce asibintin genaral. Bayan an masa 'yan gwaje-gwaje suka ce kwantar dashi zasuyi, bayan sun basa gado aka d'aura masa k'arin ruwa,mik'ewa Zarah tayi bayan likitocin sun fita,ta ce"Hanne yau na makara zan wuce Allah ya k'ara sauk'i" ta ce"to yanzu idan ya farka mai zan bashi? ni tsorona d'aya ma kar likitan nan ya cika mana kud'i kin ga dubu biyar Habu ya ba mu." Ta ce"ki tambayeshi idan ya farka shi kansa ba zai rasa kud'i ba kin dai san halinsa sarai." tana kaiwa nan ta wuce,mutane sai kallonta suke ganin yarda take tafiyar maza wasu har dariya suke hakan bai dameta ba ta sami d'an a cha'ba ta hau ta wuce." ........................... "What!?Daddy kasan abin da kake fad'a kuwa?" Murmushi yayi ya ce"na sani Ahamaduna kuma nasan kai bazaka bani kunya ba zaka iya sai ma ka fini iyawa." Girgiza kan shi Ahmad ya ke ya ce"Don Allah Daddy ka dena wannan maganar please." Murmushin yak'e Daddy yayi ya ce"Ahmad ni kad'ai nasan yarda nake ji ban san mai yasa mini hakan ba ko iyayenka na kasa sanarwa amma ina jin jikina wani iri." Hannayensa duka biyun Ahmaf ya rik'e ya ce"babu abin da zai sameka Daddy abin da kake d'aurani a kai yafi k'arfina bazan iya ba." wani murmushi yayi tare da shima rik'e hannayensa da kyau ya ce"zaka iya Ahmad." sosai jikinsa yayi sanyi,duk maganar nan suna yinta ne lokacin da Ahmad shi da mutane da yawa suka rako Alhaji Mahmud mai abaya da matemakinsa da wasu manya a k'asar nan Air port domin zasuje wani taro ne Abuja shugaban k'asa da kansa ya kirayi duka gwamnonin k'asar nan. Ahmad yaso raka mahaifin nasa sai ya nuna masa babu yuwur hakan,haka suka shiga jirgi shida wasu manyan mutane da 'yan sanda da dama,Ahmad shida matemakin mahaifinsa basu koma ba sai da sukaga jirgin ya tashi sannan suka wuce"a duk lokacin da Ahmad ya tuno maganar mahaifinsa sai hawaye sun zubo masa gashi haka kawai yaji jikinsa yayi sanyi sosai,masallaci ya wuce domin sallar magrib sai da yayi isha'i sannan ya shiga gida domin ya d'auki Hafsat su wuce" Dukansu suna zaune parlour suna kallon labarai,dai-dai shugowarsa aka nuno abin da gaba d'aya ya tayar musu da hankali a BBC News,lokaci guda Hajiya Batula Hajiya Anty da Hafsat suka mik'e Ahmad kuwa mutuwar tsaye yayi.... .[10/11, 6:22 AM] Sadfat: *SANDAR MAKAUNIYA...!* _Sabon salo._ _GAWURTATTU BIYAR TAKU NA✌️._ *UMMU AFFAN.*🤏 🅿️ 1️⃣1️⃣ & 1️⃣2️⃣ ...Ba komai ba ne sai ganin jirgin da su Alhaji Mahmud mai abaya suka hau a tafiyar da su ka yi, Ya fad'o daga sama ya k'une wanda ba asan dalilin hakan ba, kafin ya yi wani k'wak'k'waran motsi sai jin muryar mutane suka yi a waje, ana ta hayaniya. Mataimakin gwamna ne Alhaji Sani ya shugo hankalinshi a matuk'ar tashe domin mutum ne mai adalci kusan duka halayensu d'aya da mahaifin Ahmad. Da sauri Hajiya Batula ta k'arasa gaban shi. Cikin wata irin murya ta ce "An ciro su?" Ta fad'a cikin kuka. Hawayen da ke zubo mashi ya sa hannu yana gogewa, ya kasa magana hannun Ahmad kawai yaja suka fita. Hajiya Batula kuka ta fara tare da zubewa a gurin jiki a sanyaye Hajiya Anty ta k'ara so gurin itan ma kuka take ta dafa ta sukaci gaba da kuka. Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, kullu nafsin za'ikatul maut dukkan wani mai rai mamaci ne Allahu akbar sanadiyyar hakan Alhaji Mahmud mai abaya da duk wanda ke cikin jirgin Allah ya amshi rayuwarsa, duka jahar Katsina tana cikin wani yanayi na alhini harma da gwamnatin tarayya da sauran jahohin Nigeria domin shid'in ya yi suna wajen aikin alkhairin da ya kewa jaharsa, lokaci k'ank'ani gidan gwamnati ya cika mak'il da mutane manyan k'asar nan da sauran mutane. Ahmad kuwa ya zama kamar mutum-mutumi shi dai gashi nan ba ummm ba uhmmm uhmmm aka ce kukan zuciya yafi na fili ciwo, to tabbas Ahmad kukan zuci yake. Haka aka suturta duk wanda ya rasu aka kai su gidajensu na gaskiya, Allahu akbar duk wanda ya mutu shi kenan kuma sai addu'a amma a wannan lokaci jahar Katsina tayi sanyi tayi shuru duk inda ka ratsa maganar mutuwar ake kowa matan alkhairi suke masa domin a tarihin jahar ba'a ta'ba samun gwamna mai adalci irinsa ba. Hajiya Batula da Hajiya Anty suna cikin wani hali duka dangi da 'ya'yansu dake gidajen mazajensu sun zo haka surukarsu Hafsat, gidan har akayi kwana goma bai rabu da jama'a ba har akayi arba'in, tuni kuwa mataimakin gwamna Alhaji Sani ya maye gurbin gwamna yana rik'on kwarya kafin ayi za'be. Ahmad bayan nan sai da aka kwantar dashi asibiti saboda bai magana kallon kowa kawai yake yi amma daga baya ya dangana, don yasan mutuwa dole ce tana kan ko wanne bawa. ........................... Sosai ake shagali, buzumin Sa aka yanka aka gasa shi tare da shimfid'eshi saman wani babban tebur ga kayan shaye-shaye wato lemuka na kwali da na robobi dana kwalba kala-kala, babu abin da ka ke ji sai sauti mai sanyi yana tashi. Alhaji Kabiru Tafida kenan da mutanansa suna murnar mutuwar gwamna mai ci a yanzu inda ya shirya musu wannan liyafar domin nuna tsantar murna da farin cikinsu, babu abin da suke sai dariya Alhaji Mudi ya rad'a masa a kunne cewa"Mutumina babu babban shege irinka." Cikin farin ciki da fara'a ya ce"Ni d'in ai ba na wasa bane, Wallahi faɗa da aljani babu ƙyau, duk wanda yaci tuwo da ni daman ya tabbatar miya ya sha. Dole ne nayi gwamna ko ank'i ko anso sai naci, kai bari kaji wallahi akan siyasar nan babu abin da bazan iya ba dole ne na yad'a manufata." Tafawa su ka yi suna sakin dariya, tare suka mik'e gaba d'aya kowa da k'aramar wuk'a da chokali mai yatsu a hannunsa suka zagaye teburin da ke da wannan gasasshen San. Ɗaga hannu sukayi da cewa"PRP koresu PRP koresu PRP sai ta korasu ko basa so." suka saki dariya mai k'arfi sannan suka fara yanka suna ci cikin tsantsar farin ciki da annashuwa. Da haka wannan taro nasu ya k'are cikin farin ciki. Rihah ce zaune a parlour ta takure abin duniya duk yabi ya isheta domin cikin kunnanta taji abin da ya furgita tunaninta wai da sa hannun mahaifinta aka saka bom a jirgir da gwamnan jahar nan. A duk lokacin da ta tuno wannan mitin da mahaifinta ya yi da wasu mutane sai gabanta ya fad'i, sannan ta saki kuka wannan wacce irin rayuwa ce har kasa a kashe rai haka kawai saboda mulki da siyasa tabbas mahaifinta yana da tarun zunubai masu yawa, wayarta ta d'auko da niyyar kiran Yayanta Saif da sauri ta fasa domin tuno halinshi kusan d'aya da mahaifinsu idan ma ta fad'a masa tasan asiri zai tona mata, kanta ta saka tsakankanin cinyarta tana kuka sosai. Umma ce ta sakko daga sama bin 'yar tata tayi da kallo tana girgiza kai, ta k'arasa kusa da ita tare da zama, da sauri Riha ta bud'e ido jin motsi. Tana ganin Umma ta fad'a jikinta tare da sakin kuka, Umma ta fara shafa bayanta alamar rarrashi dacewa"Haba Riha ya kike son jefa rayuwarki cikin wani hali har ki haifarwa da kan ki damuwa?" cikin kuka ta ce"Umma me yasa kika kasa fahimtata? Ya dace ace kece ta farko da zaki fahimce ni da amshi uzurina.'' Ta ce"Akan wanne irin dalilin? Rihah idan kina son kwanciyar hankali to ki fita daga sabgar mahaifinki! i Idan ba haka ba kuwa wallahi zaki sha mamaki ni dai ba ruwana na sanar miki" Hawaye masu zafi suka gangaro a kuncinta gyad'a kai kawai tayi alamar "To" domin ta kasa magana saboda damuwa da takaici. Umma ta fara share mata hawaye ta ce"Ki fara shiri kin san dai jibi zaki koma England" ta ce"To Umma." Da haka ta tashi tabar gurin zuciyarta cike da zullumi. .............................. Musa sosai ya sami lafiya domin yana farkowa ya fara zage-zage sai da Hanne ta rik'eshi, ya ce"Kai lafiya wa ya kawo ni nan?" Abin da ya faru ta sanar dashi ya ce"wallahi tallahi bazan rabu da shi ba sai na rama ki kiramin likitan su sallame ni" Dai-dai nan Zarah ta shugo hannunta d'auke da take away guda biyu sai lemun kwalba biyu da kankana da ta saya aka yanka mata. A jiyewa tayi tana kallonsu,"Hanne me ya faru ne?" ta ce"Daga farkawa ya fara zage-zage kinsan dai halinsa wai sai yaje ya rama" ta ce"Ai da kin barshi, kai yanzu bayan wannan bugun mutuwar da suka maka kake son komawa tabb, ni dai ga abin da na kawo muku nan kuci muje ka biya likitoci kud'insu kafin ka tafi'' Da sauri ya zaro ido"Daman baku biya su ba?" Hanne ta ce"Da me zamu biya su?" Bai ce komai ba suna cin abincin Zarah ta ce"Bari na koma ni idan kun gama sai kuje ku biyasu kun ga lokacin tashina baiyi ba daman nazo na kawo muku na koma ne." Duka suka amsa da"To ta fita tana bonsewa, Suna gamawa Musa ya kalli Hanne ya ce"to Hanne idan kin shirya ki tashi don wallahi guduwa zanyi ko sisi bana magani." Hanne ta sake tura dubu hudun nan a ha'bar zani domin da duba daya suka yanki kati sauran canjin Zarah ta fita dasu k'ila dasu ta musu wannan siyayyar,ta ce"to amma idan suka kama mu fa?" ya ce"ke dai idan zaki gudu kizo muje" bayansa tabi sukawa yi waje da yake su uku ne a d'akin masu lalurar biyun duk bacci suke su kuwa 'yan jinyar suna waje, da haka suka samu suka bar asibitin. Suna fita suka fara gudu kai da ka gansu ka ga munafukai, da haka suka koma gida bayan sunyi nisa da asibitin suka sami keke napep suka koma. Sosai Hanne ke murna ganin ta sami kud'inta har dubu hud'u lallai tana cike da farin ciki da murna hakan yasa bayan ta tabbatar Musa ya fice ta je shagon Bala me kanti ta sayi katon buredinta ta sayi lipton milo madara da siga sannan ta sayi kwai guda biyar, sai da ta k'arar da dubu biyu sannan ta dawo cike da murna tasa ruwan zafi tana wak'arta"Ladi mai kid'an kwarya asha kid'a asha dad'i ari!!!waiwaya baya ari!!!ta saki dariya tare da turo mazaunai baya ta buga cinya tace"Ari!!!Hhhhh ta 'ba'b'aka dariya,haka tasha abin ta ta more tana jin dad'inta. .............................. Wani muhimmin zama 'yan majalisa sukayi akan wannan za'be da zai gudana Ahmad zai fito a matsayin d'an takarar gwamnar jahar Katsina a jam'iyyar ANPC inda sukayi tunanin ya cance Anta kuma yaro ne mai dattako domin tun bayan rasuwar mahaifinsa mutane da dama suke masa tayin yayi siyasar,haka a gidajen Telavision da Radio babu maganar da ake sai suna son Ahmad Mahmud mai abaya A.M.A ya fito a d'an takara suna son shi suna goya masa baya. Wannan lamari yazo wa Ahmad tamkar a mafarki, sosai abin ke basa al'ajabi sam tun da ya ga mahaifinshi ya rasu ya cire wata siyasa da burin da mahaifinshi ya d'aura akan sa, har gida wasu k'usa a jahar suka kawo masa ziyarar ban girma da bazata da kuma mik'a k'ok'an bararsu akan ya tsaya a d'an takara,da kuma k'ara masa ta'aziyya,yayi farin ciki da zuwansu sannan ya ce"zaiyi tunani,mahaifiyarsa ya sama da maganar ta nuna farin cikinta ta masa fatan alkhairi,ya ce"Mum da ni bazan amince ba ina tsoran siyasa" murmushi tayi tace"Ahmad a lamu sun nuna cewa baka son mulki, kuma irinku ne ya dace ku mulji ƙasa da jaha, sannan tabbas daman ai ba wanda yake so ya da ce yayi mulki ba wanda mutane suke so shi yadace." Ya ce"amma Mum baki ganin nayi k'ank'ata da wannan muk'amin?",ta ce"Saura kad'an fa kayi arba'in ko ka manta ne?" girgiza kai yayi yana murmushi da cewa"A'a" ta ce''to zaka iya nasanka da adalci, ina maka addu'a da fatan alkhairi a duk kan abun da kasa gaba." "To na gode Mum,Allah ya k'ara girma" ta amsa da "amin" sannan ya mata sallama bayan yaje sun gaisa da Hajiya Anty ya wuce. Alhaji Sani wanda a yanzu shine gwamna,yayi farin ciki da hukuncin da 'yan majalisa suka zartai domin shi kansa ya ta'ba tunanin hakan balle da ya tuno irin burin da mahaifin Ahmad yaci akan sa duk kan siyasa sai ya bada kai buri ya hau yayi fatan alkhairi domin yasan Ahmad zai fi shi adalci sosai ya k'arfafa masa gwiwa akan hakan. Hafsat kuwa k'awayenta ta gayyato domin atayata murnar mijinta zai yi takarar gwamna sai wani felek'e take da nuna yanzu ina ta zama matar gwamna domin haka dole tun yanzun su fara bata girma,babu abinda kakeji idan ba tashin kid'a ba,haka sukaci suka sha sannan ta sallami kowa ta gyara gidanta ta saka turare sannan ta saki wak'ar Umar M Shareef ta bazan rayu in babu ke ba,baitin take " _Kaine masoyi na farko,Idan babu kai gani fanko,Kai zana damawa koko,Kasha da dad'i a k'ok'o,Idan na shige ba fitowa ni amarya ohla shakka kai zana cewa angona_. Sosai take jinta cikin nishad'i gani take kamar gata can ta zama matar gwamna har ta hangota tana magana saman munbari ga maza da mata turmus a k'asanta sai tafa mata suke,wani ihun dad'i ta saki duk da ita ma mahaifinta babba ne domin ita ma d'an siyasa ne mahaifinta a can jahar Kano iyayenta suke karatu ne ya had'asu da Ahmad har sukayi soyayya daga k'arshe ta kaisu ga aure. Dai-dai lokacin da tayi ihun nan Ahmad ya shugo da sauri ya k'arasa ya d'auka ko wani abunne ya sameta,sai ganinta yayi tana tik'a rawa,sakin baki da mamaki yake dubanta,tana ganinsa ta k'araso da sauri ta rungumesa tare da d'aga hannunsa ta shiga k'asa ta juya,murmushi yayi ya ce"Hafsat na lura kina cikin nishad'i?" kashe sautin tayi sannan ta dawo ta rungumesa ta ce"sosai kuwa,ina cikin murna da farin cikin mijina zaiyi takarar gwamna." Zuba mata ido yayi har sai da ta hura masa iska tana d'aga kai ta ce"ya lafiya?ya ce"Mulki fa abu mai girma ne Hafsat ke baki min hangen halin da jan shiga ranar gobe k'iyama idan banyi adalci ba kawai ke hangenki na duniya ne" ,Kwantawa tayi jikinsa tana shafa kwantaccen gashin k'irjinsa ta ce"nasan mijina mai adalci ne in sha Allahu zakayi adalci" shafa gefen fuskarta yayi yace"idan ma an za'beni kenan?tace"zama a za'beka kana da farin jini fa Nawan,jan kumatunta yayi dacewa"bari na watsa ruwa"ok muje na taimaka maka"baiyi musu ba ta fara cire masa takalmin k'afarsa sannan ta zame wandon shi kuma ya cire rigar,dagashi sai boxer da singlet,tasowa tayi ta k'amk'ameshi tana sakin ajiyar zuciya idanuwanta kuwa tuni suka cenja kala domin Ahmad badai k'ira ba mutum ne cikakke da ko wacce lafiyayyar mace ta kallesa sai taji wani abu ga kamala da kwarjini,ta ko ina take aika masa da sak'on ninta inda shima ya d'auka,daga nan suka cilla duniyar ma'aurata. ................................. Wannan lamari sosai ya tada hankalin Alhaji Tafida ya ce"wannan rainin hankali na majilisa har ina me yaro kamar Ahmad zai iya a siyasar k'asar nan?! Alhaji Mudi ya ce"sannan yaro ne da ya karanci wannan harkar ta siyasa wallahi kanaji ko har yafi ubansa k'warewa kasan ita kuma siyasa iyawa ce wallahi ya tafi da hankalin mutane da yawa,idan kaji yarda yake sarrafa maga wallahi ko kai saika sallama masa jiya akayi hira dashi gidan Radio kai kaji tsari da iya zance na siyasa?Sosai idanuwan Alhaji Tafida suka fito yace"ai jin da nayi ne yasa na maka maganar amma idan yasan wata bai san wata ba,wallahi sai nasa mutananmu sun je gidajen Radion sun zauyano k'arya da k'arerayi nasa wasa ne yanzu muka fara Siyasar wallahi sai na zubar masa da duk wani k'udurinsa. ..................... Saif ne kwance bisa kujera a k'asar ta England gefe da gefensa mata ne su biyo turawa babu abinda suke bayan ta'ba ko wanne 'bangare na jikinsa ya tsotsi wannan ya juyo ya tsotsi wannan haka suke cikin wannan mugun halin ga kwalaben giya reras gabansu,dai-dai shugowar Rihah tana ganinsu a haka ta saki k'ara da kuka gaba d'aya suka dawo haiyacinsu...... [10/11, 6:25 AM] Sadfat: *SANDAR MAKAUNIYA...!* _Sabon salo._ _GAWURTATTU BIYAR TAKU NA.✌️_ *UMMU AFFAN.*🤏 🅿️ 1️⃣3️⃣ & 1️⃣4️⃣ ...Gurin ta duk'e tana ci gaba da kukanta mai ban tausayi, da sauri ya sallame su tare da k'arasowa gabanta, ya ce"Am sorry my Sister!" Hawayenta bai dai na zuba ba ta d'ago jajayen idanuwanta ta ce"Haba Yaya Saif, wannan ba al'adar duk wani d'an musulmi bahaushe bane, me yasa ka ke son 'batawa zuriarmu suna?" Hannu yasa tare da d'agota tsaye ya ce"Bazan sake ba kin ji 'yar k'anwata." Hawayenta bai dai na zuba ba ta ce"Na nawa kuma? Sau nawa ka ke cewa ka bari kaci gaba. Kuma ni dai addu'ata a kullum Allah ya shirya min big bro d'ina" Hannu yasa ya share mata hawaye ya ce"Yawwa sis addu'arki nake buk'ata." A kwatinta ya fara ja hannunshi rik'e da nata zuwa bedroom d'inta, bakin bed ya zaunar da ita shima ya zauna tare da cewa"Ya kika baro mutanan Kt?" ta ce"Kowa lafiya suna gai sheka" D'an murmushi ya yi"Ok ina amsawa, kici abinci ki huta Sis bari na wuce School." "To Yaya sai ka dawo" Fita yayi ita kuma ta cire hijabinta tana linkewa a ranta tana nemarwa Yayan nata shiri domin abun nasa yayi yawa. *KATSINA Ta dikko d'akin kara.* "Wai ni Hanne lafiya kuwa tun da na dawo aiki na lura yau kina cikin farin ciki?" Murmushi tayi ta ce"Yo ke Zarah da so ki ke kullum ki din ga ganina cikin bak'in ciki to aniyarki ta biki." Ta ce"Dad'ina da ke baki ga ne wa, ke 'yar yawa ce daga tambaya kuma." Ta ce"Ai tambayar taki ce ta zallar rainin wayau." Mik'ewa Zarah tayi ta ce"Ke kika sani kowaa tashi ta fissheshi!" "Yo daman ai ko baki fad'a ba." D'aki ta shige tana cewa"Sam Hanne baki da ganewa." Daman da alwalarta sallah tayi sannan ta zauna tana tunanin su ko nefar nan ba su da ita balle kayan kallo har kayi ya rage maka zama waya kuma bata cikin ra'ayin Zarah ko Feesu da ta gani da babbar waya bata ra'ayi ko mu gani bata ta'ba cewa ba. Ta dad'e zaune kawai tunanin mutumin da suka had'u shi da matarsa take, sai yanzu take hangen rashin kamarsu da Hisham shi wancen bai kai tsayin Hisham ba sannan ya d'an fisa kaurin jiki amma ta rasa me yasa daga kallon farko ta gansa tamkar Hisham zuciyarta ta bata amsa saboda shine a zuciyarki, Girgiza kai ta fara, tare da furta "Kamarsu ɗaya, me yasa zuciyata da ƙwaƙwalwata kuke yaudarata? Shin aljani ne ko mutum? Tambayar da kullum sai ta aiyanata a zuciyarta sai dai bata da amsarta." Shuru tayi karon farko da tayi tagumi wacece ita? Su waye iyayenta? Wato Musa da Hanne abin da ya fad'o mata a zuciya kenan. Gyara kwanciya tayi da niyar da safe ta tambayi Hanne, kamar kullum Hisham ta gani tsaye gabanta ya ce"Zarah me yasa kike wannan tunanin haba ya masoyiyata! Ba na son ganinki cikin damuwa sannan bana son ki tambayi Hanne ni da kaina zan sanar miki ko ke wacece kin san dai Hanne ita ce mahaifiyarki." Zuba mashi ido tayi tare da tashi zaune ganin haka ya k'araso gareta tare da zaunawa kusa da ita ta ce"Hisham me yasa baka son na tambayeta?" Rik'e hannayenta ya yi cikin nasa yana murzawa ya ce"Ni nasan dalilin nasan abin da ke baki sani ba don haka ki bar komai a hannuna." "To waye kai?" Murmushi ya yi"Zaki sani duka idan lokaci yayi Zarahta" Sadda kai k'asa tayi tana tunanin wannan curarran abu kuma chakuɗaɗɗan al'amari. Hannu yasa ya d'ago fuskarta tare da girgiza mata kai, ya had'e fuskarsu saitin bakinta ya ce"Zarah ina sonki soyayyar ta jazamin abubuwa masu girma akan soyayyarki na shiga had'ari mai wuyar fita wanda har yanzu nake cikinsa, Zarah kema ki soni ko kad'an ne." Kasa magana tayi sai bin shi da ido domin yanzu ji tayi kamar an d'aureta, zubawa bakinta ido yayi ya ce"Bakinki yana da kyau Zarah ina son shi sosai musamman lifs d'inki masu taushi" A hankali ya kai bakinshi cikin nata yana tsotsa hannayensa saman nonuwanta yana murzawa, ko k'wak'k'waran motsi ta kasa sai dai jikinta da takeji gaba d'aya ya saki wani irin yanayi take jinta mai wuyar fassara wanda bata ta'ba jin makamancin irin na yau ba, sosai hankalinta ya tashi gashi ta kasa magana musamman kan nipples da yakewa wani mugun tsotsa da yasata jin zafi amma ta kasa tanka mashi ,"Zarah! Zarah!! Zarah!!!" Muryar Hanne ke kiranta sai gani tayi 'bat Hisham ya 'bace a d'an razane ta juyo. Hanne ta ce"Wannan wanne irin bacci ne kike Zarah goma ta wuce ko bazaki wajen aiki ba ne?" Zarah da taji kanta na wani irin sara mata ta ce"Hanne bana jin dad'i yau ba zani ba.! Hanne fita tayi tana "To Allah ya sawak'e gashi ni ko taro da sisi bani dashi balle na siya miki ko Panadol ne na nera goma to bani da kud'i Allah ya baki lafiya." Bargo Zarah ta jawo ta rufe jikinta sosai take jin sanyi jikinta sai rawar sanyi yake, sannan babu abin da k'irjinta yake irin bugawa da ta tuno abin da Hisham ya mata yau sai ta k'ara k'amk'ame jikinta da k'yar tayi sallah ranar. (Baku tunanin abin na Zarah ko harda rashin sallar asuba a lokaci? To Allah ya kyauta, Muje dai zuwa🙊). Tana kwance nan har Feesu da wata k'awarta Nana suka shugo, ganinta lilli'be Feesu ta ce"Zarah lafiyarki kuwa?" Cikin rawar murya ta ce"Feesu zazza'bi nake." K'arasowa tayi tare da ta'ba jikinta ai kuwa zafi sosai ta ce"Allah sarki sannu, bari na amso miki magani." Tare suka fita da Nana saj gata da Malam Shehu mai chemis, dubata ya yi sannan ya ce"Za a mata allurai ne da magunguna." Idan kuma da hali ma har ruwa sai an k'ara mata domin taji k'arfin jikin, ba musu Feesu ta basa kud'in da za'a buk'ata ta ce Ya je ya kawo ya sa mata." Mintoci kad'an aka mata duk wani abin da ya dace wani wawan bacci mai nauyi ya d'auketa. Habu da ya shugo da yamma sosai yaji tausayinta shi mutum ne da ke son 'yan uwanshi sosai yana son Feesu da Zarah matuk'a komai zai iyayi akansu in har yana da halin da zaiyi hakan, shaye-shaye ne kawai illarsa da sara suka ko da yake babbar illa ce, ganin halin da take ciki sosai ya tausaya mata fita yayi ya sayo mata kayan shayi da na marmari har da rabin kaza ya kawowa Feesu wacce yau ta kasa fita ganin 'yar uwarta babu lafiya ta zauna domin ta kula da ita. Sosai take son Zarah a cikin zuciyarta tana son ganin suna kwana tare amma bazata iya ba saboda dole ta fita domin idan bata fita ba babu ta yadda za'ayi ta sami abin da zata ci amma har cikin zuciyarta bata son barinta ita d'aya a d'akin. Habu ma zaunawa ya yi har lokacin da Zarah ta farko ba laifi jikinta yayi sauk'i don sai zufa take, Feesu ganin ruwan ya k'are taje ta kira Malam Shehu yazo ya cire mata ruwan sannan ya bata wasu magagungunan sannan ya musu sallama. Abinci ta bata bayan ta wanke mata bakinta kasa ci tayi Habu ya ce"Ki had'a mata tea ko zata sha" Ganin suna da ruwan zafi sai ta had'a mata shi d'inma da k'yar tasha kusan rabi sannan tasha magani ta koma ta kwanta. Habu tashi yayi ya fita ita kuma Feesu ta gyara d'akin. Musa ne ya shugo yana k'walawa Zarah kira, Feesu ta fito ta ce"Bata lafiya." Zaro ido yayi ya ce"Bata lafiya kuma mai ya sameta?" "Zazza'bi ne ke damunta." Ya ce"Assha-assha to Allah ya k'ara lafiya." Hannu yasa aljihu sai ga nera ashirin ya ce"Gashi mik'a mata ta sayi panadol tasha Allah ya bata lafiya. Girgiza kai Feesu tayi ta ce"A'a ka rik'e kasha sigari ta riga tasha magani" ya ce"Kin gani ko, Nafisatu ke baki neman albarka ne?rainawa kika yi kenan? Ke idan ba ma don Zarah ce ba lafiya ba zan kulaki ne? To ita d'iyar albarka ce tana k'ok'arin faranta min shiyasa na bata ta sayi magani." Ta ce"To bata so ka rik'e abin ka." Ta na fad'a ta shige ciki ya tsaya nan yana jaraba. Hanne ta fito daga d'aki"Wai lafiya Musa kai da waye?" Ya ce"ni da wa fa bayan wannsn 'yar iskar 'yar taki Nafisatu wai nabawa Zarah nera ashirin a siya mata magani take min rashin kunya." Ta'be baki tayi"to ina laifi nima nace da ina da nera goma da na bata ta saya ka bata ashirin ai kuwa ta sayi magani." Ya ce"to rabu da gantalalliyar har zata gaya min maganar banza." Mik'a hannu tayi ta ce"kaga bani na aika a siyomin omo nayi wanki." Ya ce"kunji wata jaraba kuma omon ashirin zai isheki wanki to nak'i tun da bata amsa ba gara na rik'e sun k'ara auki." Yana fad'a yayi wucewarsa Hanne ta ce"kai ne matsiyaci ni nafika arziki." Mtsuww!taja tsaki tare da shiga cikin d'akin Feesu zaune ta raba kazar da Habu ya siyo ma Zarah tana ci, ganin kaza da sauri ta k'arasa tare da samin guri ta zauna ta ce"Allah sarki Nafisatu kinata k'ok'ari da k'anwarku wallahi aiyuka ne suka min yawa ban shigo ba sai yanzu" d'aure fuska Feesu tayi da cewa"to naji." Hanne ta d'an sosa kai ta ce"bacci ma take"eh" Feesu ta amsa, ta sake cewa"uhmmm nama kike ci?" Idanuwanta k'ur a kai "eh kuma bazaki ci shi ba." D'aure fuska Hanne tayi ta ce"dad'ina dake Feesu rowa waini uwarki kikewa to idan banci ba ubanwa kike so yaci?" ,Feesu ta ce"shima uban nawa bazan iya basa ba." Sakin baki tayi dacewa"Feesu!"Feesu!!"wallahi Feesu ki kuka da kanki uwwarki ce ni fa kazar banza kashi fa zakiyi da kinci"ta ce"to wai ina ruwanki ne?nima kazar nan Habu ya sayawa Zarah shine fa na d'an yanka ina ci shine." Hanne da sauri ta jawo ledar ta ce"ke kinci ubanki daman bake kika saya ba kike gaya min maganar banza." Ta yagi cinya a baki cikin tauna ta ce"Zarah da ko tashi tayi bazata iya ci ba tun da bata da lafiya" sakin baki Feesu tayi kamar zata bigeta saboda haushi. ........................... Sosai ake ta watsa mutane gidajen Radio suna zagin jam'iyyar ANPC da cewa Matashi kamar Ahmad Mahmud mai abaya babu abin da zai iya yiwa jahar nan ubansa ma me yayi balle d'ansa don haka kar a kuskura a za'beshi. maganganu dai iri-iri irin dai na hamayya da neman za'be da kuma neman farin jini, haka mutanan Alhaji Tafida ke zuwa suna kushe jam'iyyar su Ahmad da nuna kar mutane su kuskura su za'besa, wannan abu da ake yana dawowa kunnan Ahmad yana ji kuma yana gani wani lokacin abin ma dariya yake basa wannan ne yasa masa son yin siyasar gadan-gadan,shi kuwa sai ya nuna musu siyasar ma iyawa ce domin sosai yake fita tarurruka kala-kala da shiga unguyoyin talakawa k'auyayyaku duk yana yad'a musu manufarsa,sosai jama'a ke k'aunarsa domin akace idan ka iya allonka sai ka wanke siyasa iyawa ce. Tabbas a wannan lokacin Alhaji Tafida ya fara shiga rud'u ganin yadda yaro k'arami ke juya masa k'wanya amma idan yasan wata bai san wata ba,shi ta k'ark'ashin k'asa zai biyo masa. Yarda Alhaji Tafida ya rud'e zai baku mamaki musamman da yaga za'ben nan k'ara kusantowa yake. 'Bangaren k'arshe ya nufa jikinsa har rawa yake ya bud'e ya shiga,kamar kullum yauma Hajiya Falmata tana parloun cikin shigarta ta alfarma duk irin kuncin da take ciki hakan baisa ta zauna da datti,kallonta ya shiga yi idanuwanta cike da ruwan hawaye ta ce"siyasa ko ina rok'on Allah ya k'ara maka k'aunarta da sonta ita siyasar sannan ina rok'on kar Allah ya d'auraka a kai Allah ya saka maka sonta kar ya baka daman wanda yake so bashi ya cencenta yayi ba,wanda baya so mutane ke sonsa shi ya dace da mulki." Saboda rud'ewar da yake ciki bai iya tanka mata ba d'akin duhunsa ya nufa har yana tuntu'be ta bisa da wani mugun kallo na tsantsar tsana da nadamar saninsa da tayi. Komai nasa ya kusan tsayawa chek,cikin muryarsa kamar kullum dodon ya ce"Tafida kana cikin matsala fa muna buk'atar jini koma na waye idan ba haka ba komai zai tsaya sannan kai da mulki kuma har abada!!!" Dodon ya ƙare magana cikin sauti cikin rud'u ya ce"ayi hak'uri za'a kawo." Fita yayi a rud'e ya wuce Hajiya Falmata nan,bayan fitarsa Alhaji Mudi ya kira cewa ya bada kwangilar satar yara kamar guda goma ko biyar dodo na buk'atar jini,ya ce"to,bayan ya rufe gidan ya koma gidansa Hajiya Umma ta bisa da kallo ganin yanayin da ya shugo ya ce"bana son takura hutu nake so na awa biyu sannan ya wuce sama" Ta'be bakinta tayi aranta ta ce"Tafi nono fari." Taci gaba da danna wayarta. .............................. "Haba Ahmad tun da ka fara siyasar nan yanzu naga ko ishasshen lokacina baka dashi." Ta fad'a tana sake narkewa jikinsa,hannu yasa ya d'ago fuskarta ya ce"sai kin min uzuri fa kin san yadda siyasa take." Ta ce"ada ina murna da d'okin mijina zai zama gwamna amma zuwa yanzu na fara sarewa ganin a yanzu ma baka da lokacina mai yawa, ina kuma da ka zamo gwamnan?" ta idasa cikin raunin murya,shafa gefen fuskarta yayi zaiyi magana wayarsa tayi k'ara d'agawa yayi sai gani tayi ya tashi"ok to ina zuwa" Ko kallonta baiyi ba ya fice,hawaye ne suka gangaro mata tare da d'aukar fillow ta rungume da k'arfi sosai take kewar mijinta yanzu bashi da lokacinta sai siyasarsa yasa gaba,kwantawa tayi hawaye na bin kuncinta aranta ta ce"Hafsat dole fa ki nemi mafita idan ba haka ba kuwa zaki shiga uku shi babu abinda ya shafesa,ta sake cewa"to taya ya zakiyi yanzu,ganin ta kasa gano mafita ta saki kuka tana sake rungume fillow cike da son kasancewa da mijinta.... [10/11, 3:22 PM] Sadfat: *SANDAR MAKAUNIYA...!* _Sabon salo._ _GAWURTATTU BIYAR TAKU NA✌️._ *UMMU AFFAN.*🤏 🅿️ 1️⃣5️⃣ & 1️⃣6️⃣ Alhamdulillahi jikin Zahra yayi sauk'i ta sami lafiya sosai, sai lokacin hankalin Feesu ya kwanta wacce ta share kwana biyu tana jinyar Zahran ko fita ba ta yi tana kwana tare da 'yar uwarta haka ma Habu yana k'ok'ari sosai ganin ya sama musu duk abin da ya dace suci. Musa ma kullum yana shugowa gaisheta ita ma Hanne haka don tare suke wuni da Feesu a d'aka duk abin da Habu ya kawo tare suke ci don ta ce"Ita ma jinyar take ba za a ci ba tare da ita ba. Zarah sosai taji dad'in jikinta sannan kwana biyun nan tana samin ishasshen bacci ba kamar baya ba, sannan ta dai na ganin Hisham ko don saboda allurar baccin da ake mata ne oho!domin Malam Shehu idan yazo yana mata yace"harda rashin samun barci mai yawa yasata halin da taje ciki,suna zaune da Feesu wacce ta k'wad'a mata k'wad'in rama wanda yaji k'wuli da maggi harda suger kad'an domin ya k'ara almashi sosai kuma taji dad'in kwad'on tana ci a hankali,Feesu ta dubeta tace"Zarah mai yasa baki samun barci?,kallonta tayi kafin tace"mai kika gani?,"Ina tambayarki kina tambayata,to Malam Shehu yace ciwonki harda rashin barci Zarah me ke damunki da kika kasa sanar mini ko Hanne?,shuru tayi kamar zatayi magana sai kuma tayi shuru Feesu tace"wa kike dasu da zaki fad'awa matsalarki bayan mu?,Zarah tace"nifa babu abinda ke damuna inayin barcina,da banyi zaki ga inayi yanzu?,tace"amma yanzu harda rashin lafiya ke saki barci da allurorin da ake miki",Zarah tace"to ni babu komai kawai dai shawarar da zan baki ki dinga kwana gida" Harara Feesu ta wurga mata tace"da kin fad'a min matsalarki to da sai na duba inda ya dace na temaka amma tunda kin ki sanar dani to ke baki isa kisani kwana gida ba saboda idan ban fita ba ke zaki ciyar dani?,tace"Feesu ba lallai sai kin ba gardawa kanki bane zaki sami kud'i ki nemi aikinyi mana ko aikatau kikayi zaki ciyar da kanki ni da nakeyi dame kika fini?" tace"nafi ki kuwa domin ni kullum zan sami kud'i ke kuwa sai wata sannan ni bazan iya aikin wahala irin naki ba,bazan iya zuwa ina baitawa mutane ba sannan a biyani,tsaki Zarah taja tace"idan baki baitawa mutane ba ai kin sakarwa k'attan banza jikinki suna murza wallahi kece babbar mai aikin wahala Feesu ina jiye miki abinda zaije yazo please ki dena wannan halkar ba hanya bace da zata 'bille miki ba." Feesu tashi tayi tace"tunda har kinji sauk'i wa'azin naki ya dawo to yau fita zanyi bazan zauna kina gayamin magana ba kamar wata sa'arki." Mik'ewa tayi tare da d'aukar bokin wanka ta fita,girgiza kai Zarah tayi tace"ke kika sani" taci gaba da cin ramarta. .............................. Saif Alhamdulillah ya kammala karatunsa cike da jin dad'i cikakken d'an jarida kenan wanda ya amsa sunansa,k'asar taso d'aukarsa aiki amma sai yace"zai je gida ya dawo sai ya fara. Domin shi kansa baya son aiki a Nigeria don a ganinsa babu wahalar da zata sashi aiki a Nigeria bashi da wannan tunanin ko kad'an yanzu ma zai koma gida ne saboda dai iyayensa su gansa tunda ya fara karatu yake England ko hutu suka samu bai cika zuwa sai lokaci zuwa lokaci,Rihah ta fisa zuwa sosai hakan yasa wannan lokacin yace zai je daga nan ya sanar musu zai fara aiki a cen,lokacinne su Rihah za su shiga SS2 to ganin cikin hutu suke sai suka taho tare bayan d'umbin alk'awarin da ya d'aukarwa abokansa da 'yan matansa da k'awayensa zai dawo very soon,sannan suka taho,tun a air port suka fara ganin dandazon mutanan da sukazo tarbarsu don motoci uku ne duk mutanan Alhaji Tafita ne,doguwar k'afarsa ya zure daga cikin jirgin zuwa matattakalar benen jirgin,iskar NIGERIA ya shak'a a hankali ya fesar da numfashi tare da bud'e idanuwansa tas,d'an murmushi yayi Rihah na biye dashi a baya har suka sakko,da murna mutanan suka taro su,fuskar nan tasa a d'aure yake takowa cike da izza har zuwa bakin motocin da yaga alamar su ake jira domin yana sakko suke kallonsa da binsa da murmushi yana zuwa aka bud'e masa baya ya shiga haka Rihah ma, sai sannu suke musu bai amsa ba Rihah ce cikin fara'a take amsa musu har suka isa gida,daga ahalin gidan suna tsaye a harabar gidan,tsoho mai ran k'arfe magajin gari haka Alhaji Tafida Alhaji Kamalu Alhaji Auwalu,matayensu da yaransu dukansu suna gurin domin nuna murna da farin cikinsu da kammaluwar katatun d'a kuma babban jika na farko a gidan. Suna parking duka aka d'unguma bakin motar,cikin takusansa na isa ya sakko ganinsu yasa shi sakin wata fara'a tare da k'arasawa gabansu,gurin Kaka ya fara nufa tare da rungumesa yana jin farin ciki,Duka aka bisa da kallo ana dariya da yawa ciki suna mamakin yarda Saif d'in ya koma girmansa jikinsa da tsayi sannan shigarsa taba kowa mamaki sai-dai da suka tuna yanayin tarbiyyarsa sai suka sallama domin kowa baida bakin magana har kuwa da Kaka domin abin nasu kamar d'aurin baki uwar sumar da ya tara gefe da gefe aske tsakiya mai uban yawa da gani bayan maya-mayan gara har da mai yake mata sabida yanayin laushi da sentsinta ta koma sak irin na k'asar da ya baro,yana shigarsa sun d'auka zasuga yasha wata shadda ko yadi sai dai wasu 'yan manzan kaya wando k'ari wanda ya matsesa sosai daga k'asa daga saman harda wasu igiyoyi ga t-shirt d'insa matsattsiya sosai ta kamasa sai ta kalminsa shima na gayu da agwogwonsa a hannu,tabbas shigar batayi kama da ta d'an musulmi ba sai-dai dukansu sunji ba dad'i aransu don naka naka ne sai dai fa ba wanda yayi magana domin Alhaji Tafida shine kawai ya isa ya zartar da hukunci a zuriarsu hatta mahaifinsu baida ta cewa.(Nasan zaku so kuji su waye wad'an nan zuriar ko?).😂 Haka yayi ta rungumarsu d'aya bayan d'aya,yaje zai rungumi iyayensa mata da sauri sukayi baya,suna amsa gaisuwarsa suna kallon junansu k'asa-k'asa,Hajiya Balaraba taja tsaki mtsuww tare da k'arasawa gaban d'anta rta rungumesa tare da manna masa kiss tace"you are welcome my son" yace"Thank you Mum" ta kama hannunsa sukayi ciki Alhaji Tafida yabi bayansu yana jinsa cikin farin ciki mara musaltuwa ganin yarda yaron nasa ya kammala karatunsa cikin nasara. Su kuwa saura kallon-kallo sukewa juna duk da haka ba wanda ko wacce tace"k'ala Rihah ta kallesu jiki a sanyaye tace"kuyi hakuri don Allah" SAnnan tabi bayansu,suma kowa wucewa yayi ciki jikinsu a sanyaye. Saif kallon iyayen nasa yake cikin farin ciki bayan ya zauna yace"sai naga komai ya cenza min ba kamar da ba,ina Abbu da Ammi da su......bai k'ara ba Dad ya d'aga masa hannu da cewa"kowa lafiya bana son ka sake tambayarsu." Zuba masa ido Saif yayi cike da mamaki zai sake magana Dad ya katse shi da cewa"nace kar inji komai" Shuru yayi ita kuwa Rihah k'asa tayi da kai hawaye na zuba. Bayan yayi wanka sannan suka ci abinci cikin farin ciki daga annashuwa sannan yaje ya gaida Kaka sun dad'e suna hira ya dawo,d'akinsa ya shiga ya duba wayarsa da ake kira,d'agawa yayi zaiyi magana Lubna ta rigasa wata budurwarsa ce 'yar k'asar Gabon ce amma tare suke karatu sosai suke shek'e ayarsu da Lubna wacce take sonsa kamar ranta cikin harshen turanci taje magana"my Saif nayi kewarka wuni guda kawai amma ji nake kamar mun kusan wata bama tare ina cikin kewarka da begenka masoyina,murmushi yayi tare da cusa hannunsa cikin sumar kansa yace"Lubna ko kwana fa banyi ba,nima ina kewarki sosai,kukan shagwa'ba tasa masa dacewa"zata biyosa Nigeria gobe"yace"no Lubna kiyi hakuri tunda nace miki zan dawo to zan dawo ne,da haka ya samu ya lalla'bata,kwanciya yayi don ya huta sai yaji mararsa na masa ciwo,tashi yayi zaune shi yasan matsalarsa domin idan har bai kusanci mace ba akwai matsala shi mutum ne mai muguwar sha'awa sosai,tashi yayi ya cenja shiri sannan ya fito,Umma na Parlour kallonsa tayi"ina kuma zaka Saif?sosa k'eya yayi yace"uhmm Umma zanje ganin gari kwana da yawa rabona da 9j" Murmushi tayi"haka ne amma tunda ka dawo ai saita isheka yau ka huta,girgiza kai yayi cikin shagwa'ba yace"ni dai ki barni Umma nifa ba k'aramin yaro bane,tace"shi kenan my son Allah ya tsare" yace"yauwa Ummana amin" ya fice da sauri binsa tayi da murmushi,Rihah da ta fito yanzu tace"Umma ina kuma Yah Saif zashi?harara ta banka mata tace"ina ruwanki ko shi k'aninki ne?,da sauri ta bi bayansa amma sai fitar motarsa ta gani,yarfe hannu tayi da jan tsaki aranta tace"Allah ya shiryaka Yaya Saifudden. ........................... "Ahmad in sha Allahu kana tare da nasara addu'a kullum cikin yi maka nake" Ya ce"Mum na gode sosai daman Addu'arku ita muke buk'ata ga nasara nan ina ta gani duk daga cikin addu'arki ne." Murmushi tayi ta ce"Ahmad kai yaro ne mai ladabi a gare ni addu'a dole ce na maka fatana dai idan ka sami mulkin nan kaji tsoran Allah kayi aiyukan da ya dace." ya ce"In sha Allahu zaki sha mamaki sai kinyi alfahari dani sai Daddy yaji dad'i sai yasan bai bar baya da k'ura ba sai yayi alfahari da samuna kamar yarda yake fad'a." Mummy ta share hawayen dake zubo mata ta ce"Allah ya maka albarka kai ma ya baka 'ya'yan da zasu maka." ya amsa da amin. Kud'i ya ajiye mata sannan ya mata sallama sai albarka take sa masa. "Hafsat ya kamata zuwa wannan lokacin ace mun sami baby boy ko girl ina son naga kin haifa min yara." Zaro ido tayi sai kuma ta rungumesa ta baya ta ce"haba my honey saurin na me haka?ya ce"ba maganar sauri ko dai zamuje asibiti ne a duba mu, jiya bakiji abin da su Alhaji Tafida suka fad'a a gidan radio ba wai taya zan iya kula da mata da k'ananun yara don ban san zafinsu ba, ban haifa ba kar talakawa su dangwala mini." Cikin kissa ta ce"to meye abin damuwa anan maganarsa cen yake idan Allah yayi fa zakayi nima haihuwar nan ina sonta." Hannu yasa yana shafa cikinta ya ce"anya a yau bazan sama mana baby ba,da sauri ta haye cinyarsa tana ta'ba sandar girmansa ta ce"gara dai hakan nan suka fara aikin romantic junansu cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa har akazo ga oganniyar, cikin wani irin salo da k'warewa yake tafiya da ita,itamma sosai ta sakar masa jiki tana aika masa da tana sak'on lokaci k'ank'ani suka fita daga haiyacinsu. .............................. Da wuri yau Zarah ta wuce gurin aiki kasancewar kwana uku bata zuwa Allah-Allah take ta tafi ga tsoran da takeji a zuciyarta,sai-dai tana zuwa taji, sai ya jiki ake mata abin ya bata mamaki taji ogarsu nacewa"Yayanki da ya nemar miki aiki ne yazo ya sanar mana baki lafiya." Baki bud'e take kallonsu sai-dai ta kasa magana, suna cikin aiki taje wani tebur sai ganinsa tayi zaune, da sauri ta k'ara Hisham ta kira sunansa, Saif wanda yazo gurin tun d'azu ya bita da kallo cike da mamaki,ta ce"Hisham wai me yasa kake bibiyar rayuwata nace maka waye kai kak'i sanar mini al'amuranka suna da mamaki." Kallon abin Saif yake kamar wata durama aransa ya ce"bari dai na biyewa wannan yarinyar k'ilan na samu na rage zafi don a mugun matse nake. Gyara zama ya yi ya ce...... [10/11, 3:26 PM] Sadfat: *SANDAR MAKAUNIYA...!* _Sabon salo._ _GAWURTATTU BIYAR TAKU NA✌️._ *UMMU AFFAN.*🤏 🅿️ 1️⃣7️⃣ & 1️⃣8️⃣ ...Ya ce"Saboda ina sonki ne!" Wata harara ta ban ka mashi da cewa" To ni ba na sonka ko ana so dole ne?" Kallonta ya yi sama da k'asa gani ya yi kamar yasan fuskar amma sam ya mance inda yasanta, sai lokacin ya lura da kalar shigarta ya ce"Wai ni da mace ma nake magana ko namiji?" Wani irin mugun kallo ta masa ba ta san lokacin da ta k'arasa gabanshi ba, har suna shak'ar numfashin juna cikin muryar maza ta ce"Dawa ka ga nafi kama?" Kusancin da tayi dashi yasa lokaci kad'an ya diriri ce abin ya tashi waigawa yayi ganin ba mai kallonsa ya zawota da k'arfi sai gata jikinsa sosai ya matse ta yana saukar da numfashi,da sauri ta turesa tana cewa"Wannan iskancin har ina bayan cikin bacci da kake zo min yanxu har a zahiri kenan?" Jin abin da ta ce ya saki wani murmushi a ran sa ya ce"Tabbas wannan za a je da ita dole na sami biyan buk'atata,"Ina ne gidanku?" Ya tambayeta juyawa tayi ta ce"Da da kake zuwa waye ya sanar maka gidan. Wata irin muguwar sha'awarta yaji ta bijiro masa murmushi ya saki yana kallonta har ta gama aikinta takama hanyar gida yabi bayanta, har sai da ya ga gidansu, tsaki yaja ya ce"Nan ne gidan naku matsiyata aiko dole ma na sami abin da na ke so tun da har naji ina sha'awarki domin babu abin da nake nema na kasa samu. Sakkowa ya yi ya tambayi wani mutum takaitaccen tarihin mutanan gidan ya sanar masa,ya basa dubu d'aya mutumin sai murna yake,komawa mota yayi yana sakin murmushi da cewa"Zarah kamar na sameki gashi sunanki ya min dad'i sunan yarinyar da nake k'auna ada sannan sunan kakata Fatima Zarah amma hakan ba zai sa nak'i cimma burina akan ki ba 'yan mata" Yaja motarsa ya wuce Club domin ya rage zafi,cen ya had'u da zafafan mata sukayi sharholiyarsu amma duk motsinsa Zarah yake hange,bai ta'ba jin irin abin da yaji ba lokacin da ya rungumeta alamu sun nuna zazzafa ce yarinyar tabbas yana son tarayya da ita. Ranar saboda giya da yasha ta masa yawa a club d'in ya kwana. ........................... Hajiya Falmata ce ke gyaran parlournta bayan ta gama ta jawo plate d'in abincin da ta ajiye a center table amma ta kasa ci sai hawaye ne ke bin gefen fuskarta idanuwanta d'aure akan k'ofar d'akin duhun su Alhaji Tafida, hawaye kawai ke zubo mata ko hannu ta kasa sawa bare ta taresu domin ko ta tare bazasu dena zuba ba ba,hannu tasa tayi tagumi hankalinta a matuk'ar tashe wannan wacce irin rayuwa ce mai cike da tarin jarabobi tabbas duniya ta lalace abubuwan dake cikinta tuni suka fita cikin ran Falmata sosai take kuka da tuno rayuwarsu ta baya mai cike da jin dadi da farin ciki lokaci guda komai ya tsaya. Alhaji Tafida shi da Mudi suka shugo,ko d'agowa batayi ba bare ta kallesu,su d'umma basu kulata ba suka shige ciki,girgiza kai tayi tana matsar hawaye Yanayin da suka ga abin tsafinsu abin ya basu tsoro,kallon juna su ka yi. Alhaji Mudi ya rikice ya ce"Me ke faruwa ne?,Da sauri Alhaji Tafida ya fara zufa sai keto masa take wata k'warya ya bud'e sai-dai ya ga abin ciki bak'ik'k'irin sosai gabansa ya buga musamman jin dodon yana amsa kuwwur kiran sunansa"Tafida!"Mudi!rayuwarku tana cikin had'ari idan har bakuyi gaggawar raba shi da ita ba, Sannan siyasarku na cikin tan'bele idan har baku rabasu ba, Sannan muna buk'atar jini!,dukansu idan ban da zufa babu abin da suke don sun kasa gane ma abin da yake nufi a raban da haka suka lalla'ba dodon cewa zasu kawo jinin sannan suka fita, har lokacin Falmata na gurin saboda rud'in da suke ciki basu tanka mata ba duk kuwa zagi da addu'ar ta'bewa da tabisu da ita, bayan sun kulle ko ina suka hau mota suka koma cen cikin gidan, dukansu shuru suka yi bayan Mudi yayi parking zuwa cen Tafida ya ce"komai zamu iya ganin ba mu samu ko wacce irin targard'a ba amma kai mai ka fahimta?ya ce"Me kuwa na fahimta duk d'aya muke babu abin da na gane" Tafida ya ce"A sato yara kai ko manya ne asamu dodo ya sami jinin kafin musan inda d'ayar maganar ta dosa" Da haka sukayi sallama. .............................. "Hafsat manyan mata matar babban mutum gwamnan gobe" Murmushi tayi mai k'ayatarwa tana wani hura hanci tana son a yabeta ko a fasa mata kai da kalamai ta ce"Shukra kenan ko baki fad'a ba maganar haka take" Shukra tayi murmushin yak'e tana bin k'awar ta ta da kallo cike da jin haushin irin jin dad'in da Hafsat d'in take ciki ta ce"k'awata kenan kina jin dad'inki fa,"To ya son ranki?" "Fari sol ai abin farin cikinmu ne ganinki cikin jin dad'i." Ahmad ne yayi sallama suka amsa kai tsaye sama ya nufa, Hafsat da Shukra suka bisa da kallo, daga bisani ta mik'e ta ce"kin ga bari naje gurin mijina, maganar gaskiya ba yanzu zan fito ba idan zaki tafi ne to ki gai da gida kin ga tafiyata" ta idasa fad'a tana hawa matattakala. Shukra ta bita da wani kallon takaici da hassada ji take kamar ta fincikota ta fad'i K'asa ta dad'e a gurin kafin ta mik'e jiki a sanyaye a ranta ta ce"wallahi duk wani shirinki ina sane kuma sai na tona asirinki" ta fice daga gidan ranta a 'bace. Ahmad babu abinda ya ke sai juyi a bedroom daga ganinsa zaka gane cike yake da damuwa, Hafsat wacce ta shugo ta dubesa cike da alamar tambaya kamo hannunsa tayi suka zauna bakin bed ta ce"Honey lafiya?me ke faruwa?,numfashi ya ja ya ce"har kar siyasa abu ne mai girma tabbas Alhaji Tafida ya d'auki abin da zafi da girman da ya wuce misali amma abin nasa yayi yawa" "Mai kuma ya faru?,bai bata amsa ba ya d'aga wayarsa ya kira number d'in abokinsa Usman wanda sukayi karatu tare da shi a fanni guda Usman d'an asalin jahar Kebbi ne amma aiki ya dawo da shi Katsina bayan kammala karatunsu, Ahmad da Usman abokan juna ne sanadiyyar abotansu karatunsu da sukayi tare jininsu ya had'u har suka k'ulla abota yanzu haka shima Umar yana da mata Zainab har da yaransu uku Jiddah Shuriem sai k'aramin Suhail,sam Hafsat da Zainab basa k'awance wai irin na matan abokan nan domin ra'ayin ko waccensu da ban Zainab tana da k'yirki sosai yayin da ita kuma Hafsat ke da d'agawa ko haihuwa Zainab tayi Hafsat daga barkar da suke zuwa da Ahmad to bata k'ara komawa bare taje suna,Ahnad yayi k'ok'arin ya had'asu ganin Hafsat bata son k'awance da Zainab sai ya rabu da ita duk da bai ji dad'in hakan ba don yasan Zainab ba dai k'yirki ba ko da girki ne ta koya amma girman kai irin na Hafsat bazata bari hakan ta faru ba. Usman ne ya d'aga kiran Ahmad. cikin wasa da zolaya yace"Ahmad gwamnanmu na gobe in sha Allah da girman kujerarka" Ahmad ya ce"duk ba wannan ba kana ina ne?ya ce"ina gida mai ya faru ne?ya ce"nazo na same ka yanzu ko zaka zo?,cikin zolaya ya ce"kai da kaji kiran manya kasan da magana to ya na iya gwamna guda dole na amsa kira" Duka murmushi sukayi sannan sukayi sallama,Hafsat tana yatsina fuska ta ce"me yasa ni bazaka sanar min matsalarka ba sai ka kirasa,? Nifa Usman d'in nan wani lokacinma haushi yake bani halinshi d'aya da matarsa." Wani kallo ya mata ya ce"aminin nawa to na gode" matsowa tayi kusa dashi tare da rik'e hannayensa ta ce "nifa ban fad'a da wata niyya ba gaskiya ce kawai" "uhmmm a wajenki ba take gaskiya" jin kiran Usman ya amsa yana fita daga ɗakin. ta'be baki Hafsat tayi da cewa sai na rabaku. ........................... A hankali ya ke gangaro da motarsa zuwa cikin layin domin duk hanyar babu kyau Usman ya ce"Ka gani ko don Allah dubi halin da talakawa suke ciki? Ahmad saboda tausayi har 'yar kwalla yayi shi mutum ne mai tausayi, Usman ya ce"dole ne fa ka dun ga basaja idan ka zama gwamnan nan domin ka din ga ganin halayen da talakawanka ke ciki domin sanin matakan d'auka domin ci gaban jaharka da kuma sauke nauyin da ya rataya akanka" Parking Ahmad yayi suka fito suna tafiya a k'asa suna kallon unguwar yadda kowa ke harkarsa daga gani kasan suna cikin kuncin talauci da tsadar rayuwa. Ahmad ya ce"maganarka gaskiya ce Usman Allah dai ya bamu ikon rik'e nauyin da zai rataya a kan mu." Da amin Usman ya amsa. Zarah ce ta fito daga gida ganin mutane tsaye k'ofar gidansu ta k'arasa, tare da tsayawa gabansu, daga Ahmad har Usman suka zuba mata ido,ganin Aliyu ya sata zaro ido tace"laaaah kai ne?,d'aure fuska yayi yana bin ta da kallo ganin shigar dai tata tana nan ta maza har maganar,ba wanda yayi magana shi dai Usman cike yake da mamakin ina Ahmad yasan yarinyar nan mai siffar maza. Zarah ta ce"kayi hakuri kwanaki na ganka nace kai ne Hisham da muka had'u ya ce ba kai bane, amma na kasa yadda kai ne dai Hisham domin ni ban fa wani banbanci da zanƙi yadda ba!" bai mata magana ba ya kalli Usman ya ce"muje" Da sauri tasha gabansu ta ce"haba Baabaa magana fa nake to mutum bai kuskure ne kuma nace fa kayi hakuri duk da nasan kaine, kana dai ɓoye mini ne saboda wancan lokacin kana tare da matarka yanzu kuma da abokinka, abin da a tarihina ban ta'ba yi ba kenan bawa wani hakuri ko da kuwa shine mai gaskiya."ya ce"ok to yayi" ta ce"amma ina wannan matar taka wacce tafika girma wallahi sam-sam-sam baku dace ba." ta fad'a tana yarfe hannu, zaro ido daga Ahmad har Usman sukayi suna kallonta, d'an murmushi tayi ta ce"ni fa bana 'boye gaskiya idan tazo fad'inta nake kowa ya sani ma" Usman murmushi ya yi domin sosai yarinyar ta burgesa ya ce"mene sunanki?ta ce"Sunana Zarah" "Da kyau Suna mai dad'i" Murmushi kawai tayi tana kallon Ahmad da ya d'aure fuska bata san me yasa ya ke mata kwarjini ba kuma haka kawai take jin tana son sa har cikin zuciyarta. Ahmad yac e"Idan ka gama sai mu wuce" Da sauri Zarah ta ce"Amma don Allah me kuka zo yi layinmu?" Wani kallo da Ahmad ya mata yasata saurin shuru Usman ya ce"Kawai mun zo ganin gari ne" ta ce"uhmmm amma don Allah uhmmm da man uhmmmmm" Duka suka zuba mata ido Usman ya ce"daman me?,ta ce"daman wai zance ne..sai kuma ta ce"ko da yake babu komai,Tsaki Ahmad yaja mtsuww tare da fuzgar hannun Usman suka wuce, murmushi kawai tayi tare da bin su da kallo har suka 'bace ma ganinta sannan ta wuce daman wajen aiki zata,ranar haka ta kasance cikin farin ciki da ta tuno Ahmad sai tayi murmushi. Usman kuwa bayan sun shiga mota ya ce"wai ni kuwa ina kasan yarinyar nan?" Nan Ahmad ke basa labari har da biyosu gida da tayi ya d'aura da cewa"Da alamar bata da hankali da tarbiyya" Usman kuwa mai zai yi ba dariya ba ya ce"kai amma wannan abu ya bada citta gaskiya zanyi abota da ita da alama kanta fa yana ja" Da sauri Ahmad ya ce"da wannan kuchakar zakayi abota baka ga unguwarsu ko gidansu bane?" Murmushi yayi ya ce"na gani mana a hakan nifa ta burgeni ne kuma wallahi kunyi macin fa" da sauri ya zaro ido ya ce"bana so Usman wannan wace irin magana ce" Sun yi tafiya har sun bar zan cen sai Usman ya tun tsire da dariya Ahmad ya ce"Lafiya?" cikin dariya ya ce"amma ina wannan matar taka da ta fika girma sam-sam-sam baku dace ba"maganar da Zarah tayi d'azun ya maimaita tuni Ahmad ya d'aure fuska ya ce"wai Usman meye hakan ne ko kaima ka koma ita ne?bai bar dariya ba har ya saukesa gida shi kuwa ya wuce cike da k'uluwa da k'udirin duk ranar da suka kuma had'uwa sai ya gyara mata zama. .............................. Cike da mamaki Zarah ta fito daga gidansu wai ana kiranta waje ita abin ma wani banbara k'wai ya mata sanin tun da take ba'a ta'ba zuwa gurinta da sunan zance ba,ita kuwa Hanne sai murna take wai 'yar tata ta fara zama mace tun da har an fara zuwa nemanta,ganin Saif cikin had'ad'd'ar motarsa abin ya bata mamaki matuk'a da gaske acewarta Hisham ne,da sauri ta k'arasa tana harararsa ta ce"wai Hisham ba nace ka rabu dani ba,murmushin yaudara yayi ya ce"da zaki kira ni da Saif ko Saifuddeen da nafi jin dad'i akan Hisham" ta ce"koma me nene ni bai dameni ba,ya ce"da zaki shugo da yafi wata magana zan miki",ba tunanin komai ta shiga motar,wani sanyi yaji aransa ya ce"yauwa ko kefa",ta ce"Sai ka fad'a,mai maimakon yayi magana sai kawai naji ya chachimeta da sauri ta zaro ido ta ce"lafiya?numfashi yake saukewa da k'yar nan take idanuwansa suka sauya kala,k'ok'arin k'wace kanta take amma ta kasa domin sosai ya matseta,jin hannunsa cikin rigarta yasata zaro ido da sauri domin tun da take da Hisham bai ta'ba zura hannu cikin rigarta ba sai yau,jin yana k'ok'arin fito da dukiyar fulaninta yasata saurin bige hannunsa amma ta kasa sosai yake chakud'asu ta kusan fita haiyacinta gashi ya had'e bakinsu sai wani fitar da numfashi yake,turesa take amma kamar tana ture dutse ta kasa, Saif kuwa tuni ya fita cikin haiyacinsa....... *Na kusa da na ƙarshe a free pages, ƴar uwa hanzarta kar ayi tafiyar gawurtattu biyar baki ciki.* [10/11, 3:32 PM] Sadfat: *SANDAR MAKAUNIYA...!* _Sabon salo._ _GAWURTATTU BIYAR TAKU NA.✌️_ *UMMU AFFAN*🤏 🅿️ 1️⃣9️⃣ & 2️⃣0️⃣ _Last free pages._😇 ...Sosai ya ke yamutsata son ran shi. Allah ne ya bata sa'a ta samu ta tunkud'esa da k'arfi domin duka jikin shi ya gama mutuwa. Bin ta ya yi da kallo kamar d'an mayu. Ta ce"Amma kai d'an akuya ne?" Sosai ya ji zafin Maganarta taya wannan k'azamar yarinyar zata kira shi da haka? Ɗaga hannu ya yi zai mareta sai kuma ya sauke da ya tuno k'udurinshi a kan ta, cikin wahalalliyar murya ya ce"Zahra kin san ina sonki fa" Ta ce"Ni kuma kasan bana sonka don Allah ka rabu dani" ya tsani ta ce bata son sa aran shi ya ce ke idan ban da ina son na huta da ke mai zai kawo ni cikin wannan unguwar taku ma balle har na kulaki baki san waye ni ba. Ya ce"Zarah komai kike so zan baki kud'i ke idan ma zaki bar aikinki ni a kullum zai iya baki fiye da abin da ake baki a duk wata ni kuma a kullum." Wani kallo ta masa ta ce"Ohh haba Baabaa" ta fad'a cikin maganar kwalawa. "Hisham ni zan wuce" ya ce"ki ce min Saif" hannu yasa aljihu ya ciro kud'i ya mik'a mata. "Ga wannan" kud'in tabi da kallo sai kuma ta girgiza kai ta ce"A'a na gode" zata bud'e motar ta fita da sauri ya damk'i hannunta yana girgiza kai ya ce"No Zarah" ta fin hannunta ya bud'e ya saka mata kud'in sannan ya manna mata kiss ya ce"Sai na sake dawowa da fatan zaki sakar min jikinki nayi yarda na ke so" Da kansa ya bud'e mata, fita tayi ta tsaya tana kallonsa har yaja motarsa ya wuce. Kud'in hannunta ta duba da ya bata kusan dubu ashirin, Feesu ce ta k'ara so tana bin bayan motar da ta ga k'anwar tata ta fito ciki sannan ta k'araso tare da kallon hannunta cikin alamar tuhuma ta ce"Zarah waye wancen?" Ɗ'an yatsi fuska tayi ta ce"Wani ne" sannan taci gaba da tafiyarta. Bin bayanta Feesu tayi, yarda ita ta lalata rayuwarta bata son ita ma Zarah ta kasance cikin irin halin da take ciki. Hanne tana ganin ta shugo ta ce"Iye-iye 'yan matan Hanne a yau na yarda mace na haifa ba mata maza ba." Feesu ta d'aure fuska ta ce"Wai Hanne me ke faruwa ne?cikin murna ta ce"Saurayi ne fa yazo yana sonta wannan abun farin ciki har ina?" Feesu ta zaro ido ta ce"saurayi kuma?kallon Zarah tayi ta ce"Zarah wallahi ki natsu karki kuskura ki biyewa samarin zamani basu da imani." Hanne ta fara tafa hannu ta ce"Yau na shiga uku bak'in ciki k'iri-k'iri ba tsoran Allah to wallahi Feesu kiji tsoron Allah ke dake da samarin kwando-kwando ita sai ki mata bak'in ciki?" Tsaki Feesu ta ja ta ce"Ke ce zance kiji tsoron Allah karki jefa rayuwar 'yarki cikin garari." Zarah ta kama hannun Hanne ta zuba mata kud'in ta ce"Ga abin da ya bani" Ai wata bud'a da Hanne tayi yasa Musa k'arasowa da sauri yana tambayar lafiya" Hanne ta ce Musa ta yani murna Zarah tayi farar k'afa tayi goshi daga zuwan farko saurayi ya bata dubu ashirin nan gaba kuma sai hamsin, ai nan fa suka kama murna harda taka rawa, Zarah ta girgiza kai kawai ta wuce ciki. Feesu ta ce"Wallahi kun dai ji kunya bamuyi dacen iyaye ba mu kam." Musa ya ce"Cen da ya warki ke dai bak'in ciki kike" Hanne ta ce"Ai kuwa kuma sai dai y'an bak'in ciki su mutu" cike da takaici Feesu ta wuce ciki tanawa Zarah masifa da fad'an karta kuskura wani namiji ya rabata da 'yan cinta mutumcinta. D'an murmushi tayi ta ce"Haba Feesu ai daman ni ba irinki bace duk abin da kike tunani ni bazan ta'ba aikata hakan ba" Wani sanyi Feesu taji aranta don harga Allah bata son rayuwar k'anwarta ta shiga irin tata rayuwar. ..................... Rihah ce zaune tayi tagumi abubuwa da yawa ne ke dawo mata, tana son ta zamo sila kuma sanadiyyar warwarar matsalar da tawa danginsu ka tutu, amma ta ina zata fara?ta tambayi zuciyarta domin abubuwan akwai rikitarwa mahaifinta yasan ita d'in tasan wasu abubuwa da yawa cikin lamarinsa amma ta inda zata fara ne matsalar har cikin zuciyarta tayi da nasanin kasantuwarta 'ya a gurinsa sai dai bata da yarda zatayi haka Allah ya tsara, shugowa yayi gidan ransa a 'bace, a hankalin ta d'ago ido ta kallesa gurinta ya k'ara so da sauri. "Sannu da zuwa Daddy" ta fad'a ganin ita yake tun karowa, d'aure fuska yayi sosai ya ce"Rihah yaushe ne zaki koma England kin san dai ko Secondary baki kammala ba" Hawaye ne suka fara zubo mata tayi k'asa da kai cikin takaici. Ya ce"tambayarki nake kin yi shuru yaushe hutunki zai k'are?" A hankali ta d'ago ta ce"Daddy me yasa ba ka son zama na kusa da ku? Ni fa 'ya macece ya dace ace ina kusa da ku" zai yi magana Saif ya shugo. Umma kuma ta sakko daga sama, Saif ya zauna kusa da Rihah tare da d'ago fuskarta ya ce"Rihah me ke faruwa kike kuka?" Kallon Daddy tayi kafin ta ce"Yaya Saif tun da ka kammala karatunka me zai sah Daddy ba xaiyi hakuri ba ni ya barni naci gaba da karatuna anan ba, ni bana son komawa ni kad'ai, ni fa macece mai yasa Daddy bai duba da hakan?" Ta k'arashe cikin kuka, duka jikinsu yayi sanyi musamman Umma ta ce"Alhaji kayi hakuri kawai ta ci gaba da karatunta anan ni bana son abin da zaije yazo" Saif ya ce"Haka ne nima abin da zance kenan tun da ta nuna bata so Daddy ka hakura kawai." Duka kallonsu yake zuciyarsa na hasala bai ce komai ya nufi sama, Saif ya fara share mata hawayenta ya ce"Kiyi hakuri Little Sis" Hawayenta sun kasa daina zuba ya ce"Rihah anya kukan nan na iyakar barinki karatu anan ne kuwa?" Kallonsa tayi Cikin zubar hawaye ta ce"Me yasa Daddy baya son barinmu k'asar nan?Yah Saif ina batun Abbu Ummi dasu Yaya Sadik? Me yasa Daddy bai son ayi maganarsu?me yasa duka 'yan gidan nan kowa yayi burus da batun?zuciyata ta kasa yarda ta kasa aminta da wannan curarren al'amarin." Ta idasa da sakin kuka, sosai jikin Saif ya yi sanyi ya ce"Nima ina tunanin hakan amma me yasa tun da Daddy baya so bazaki bar zancen ba" Da sauri ta kallesa ta ce"Ada family d'inmu ba haka suke ba, na fika sanin komai tun da na fika zama kai ko a 'yan gidan nan ba kowa ka sani ba amma ni na son kowa nafika son mutane da shiga cikinsu. Yaya Saif idan har za a ci gaba da zama a haka akwai babbar matsala" Dafe kansa ya yi ya ce"Rihah kema wani lokacin kina da matsala, wai ina ruwanki da damuwar wasu?Kiji da kanki mana" mik'ewa ya yi ya ce"Haka kawai ina cikin farin ciki kin zo zaki bani damuwa, ni dai ina shawartarki ki mance da kowa da komai idan kina so ku zauna lafiya da Daddy tun da ya nuna min baya so kin ga na sake maganar?" Hayewa sama ya yi ya bar Rihah a gurin. Binsa tayi da kallo tana share hawaye a fili ta ce"In sha Allahu sai na gyara komai ni bazan bari hakan taci gaba da faruwa ba ko da kuwa zan rasa raina ne." Ta idasa da shasshek'ar kuka muryarta cike da rauni. ........................ Ahmad yanzu abubuwa sun masa yawa ko lokacin Hafsat bashi dashi, ita kuma sosai ta damu da hakan ta kasa samun mafita tun farko da tasan hakan zai kasance da bata yarda ta k'arfafa masa guiwar yayi siyasar nan ba tun da bashi da ra a yi amma yanzu mutane sun cusa masa ra'ayin yafi damuwa da damuwar mutane akan tata shi kenan baya zama, bayan wasu 'yan siyasar da yawa kullum suna cikin ra'ba da Ac suna hutunsu sai dai su tura 'ya'yan talakawa suna wahala dasu idan sun ci kuma su mance dasu. Shi kuwa Ahmad Mahmud mai Abaya da kansa da amininsa Usman Ishak da mutanansa suke komai tare, su kan su mutane mamakinsu suke domin sam Ahmad bashi da girman kai irin na sauran 'yan siyasar k'asar nan. Kai da fata ya ke abin sa domin ganin jaharshi taci gaba, kullum kuma cikin addu'ar mahaifiyarsa ya ke ya zamo k'adangaren bakin turo kainuwa dashen Allah d'aya tamkar ya dubu Alhaji Ahmad Mahmud mai abaya, kwarjini kamala da dattako ya tarasu matashin d'an siyasa mai kimanin shekaru 40y a duniya kyakkyawa mai kwarjini mutane na k'aunarsa hak'k'un, yanzu haka za'be bai wuce kwana biyu ba za'a gabatar sosai suke yak'in neman za'be k'auyuka da burane, ga Alhaji Sani gwamna me ruk'on k'warya sosai yake ba da gudunmawarsa akan za'ben babu hassada bare k'yashi. 'Bangaren su Alhaji Tafida ma batun haka yake domin sosai suka mayar da hankali na ganin sun ci za'ben nan babu abin da yake fata da buri ganin ya mallaki jaharsa a matsayin gwamna mai ci. Duk wani fata da buri sun d'aurasa a wannan za'ben domin kallo suke ma kamar sun ci sun gama sun kayar da wannan gwamnati ta yanzu. A ranar da za'ayi za'be sosai abin zai k'ayatar da kai saboda an samu tsaro sosai duk wani abu da zai tayar da hankalin jama'a an toshe, sai hada-hada ake burin kowa ya amshi wannan farar doguwar takarda da jam'iyyoyi ke kai domin samu ya dan gwalawa wanda ransa ke so, anja layi dogo rerass na maza daban na mata daban yarda abin ke tafiya zai k'ayatar da kai sosai. Haka suma masu gudanar da al'amuran za'ben duk suna zaune kowa yana abin da ya kamata da haka ake ta za'ben. Ɓangare guda kuwa wasu mutane a 'boye suna bawa mutane kud'i da niyyar su dangwalawa jam'iyyar hamayya ta PRP kun san mutane da kud'i duk wanda aka bawa amsa yake. (Abin da ke zuciyarsu ne kawai dai ban sani ba🤪suna dangwalawa PRP ko ANPC ko kuwa wata jam'iyyar daban ni dai an hanani gani, duk wanda zai dangwala shi kad'ai yake zuwa bare na samo rahonton wanda suke dangwala mawa lolx🤪). Habu ne yake ta shiri zai fita. Zarah tazo gabansa ta zauna tana kallon abubuwan da yake ta shiryawa, sosai take kallonsa ta ce"Habu wai shirin me ye kakeyi haka?" Kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce"Zarah anjima kad'an zamu fita ne domin sace akwatinan za'be na jam'iyyar ANPC da zarar an kammala guri-guri mabanbanta aka tura ko wanne daga cikinmu, ni ne zan sace na wannan unguwar." Zuba masa ido tayi kafin ta gyara zama ta ce"Haba Habu wai mene ne amfanin hakan? Me yasa 'yan siyasar nan suke amfani da ku sannan ku kuma kuna biye musu saboda wasu 'yan k'alilan kud'in da suke baku yanzu? Da zarar kuma anyi za'be shi kenan sun manta daku me yasa bazaku yiwa kanku karatun ta natsu ba. Suna amfani da ku suna jefa rayuwarku cikin had'ari nadama da danasani" Shuru yayi sannan ya d'ago a hankali ya ce"Kusan haka ne maganarki amma ya muka iya tun da mun riga mun amshi kud'insu kawai ki basar abar maganar" ta ce"Habu ba zai fa yuwu ba" Sosai yake kallonta da kalar tata k'arfin halin ta ce"Ina so duk wad'anda za su yi aikin nan kai to ka kirasu akwai wata magana da zan muku." Ba musu ya d'auki wayarsa ya kira duk wad'anda za su yi aikin tare, kusan awa guda sannan dukansu suka taru. Wani Tsalha ya ce"Wai Baabaa me ke faruwa ne? Kasan fa muna ta shirye-shirye ne akan hark'allar nan" ya ce"karka damu Baabaa ku zauna kuji" Bayan kowa ya zauna Zarah ta fito bin ta sukayi da kallo cikin mamaki Isuhulle ya ce"Baabaa wannan mata mazar kuma fa?" ta ce"Kai dalla kama bakinka" Da sauri ya ciro addarsa ya ce"Ki mini iskanci yanzu in sassaraki." Habu ya ce"Haba baabaa yarinya ce macece fa rabu da ita" Zarah ta ce"Wai kasan ni wacece ma?" Duka suka bita da kallo gyara tsayuwarta tayi ta ce"Ni d'in nan da kuke gani babban mutum ne zai aure ni, nayi alk'awarin idan nayi aure zan baku kulawa zan samarwa ko wanne daga cikinku aikinyi in har zaku hakura da satar k'uruk'un mutane akwatin za'be" Nan fa ihuw ya tashi sai zage-zage suke Isuhu ya ce "Wannan rainin wayan har ina mu tsaranki ne ko an fad'a miki ba mu da abinyi ne?" Kasa cewa komai tayi ganin sai masifa suke, fita waje tayi duka suka biyo bayanta daidai tsayuwar motarsu Ahmad shi da Usman duka suka fito da sauri ganin 'yan sara sukar da suka biyota, tana ganin Ahmad ta saki murmushi da sauri ta k'arasa gabansa ta tsaya tana murmushi suma duka suka tsaya chek suna kallonta, cikin gadara da iko ta ce"Me na fad'a muku?" nuna Ahmad tayi ta ce"Kun ga wannan babban mutum ne yana da kud'i sosai idan kuka fasa k'udurinku to shi zai baku aikin yi da kud'ad'e domin ku gyara rayuwarku nayi muku alk'awari bayan aurena da shi zaku sha mamaki sai kun zamo abin alfahari" Daga Ahmad har Usman sakin baki sukayi suna kallonta cike da mamakin jin furucinta su kuwa abokan Habu murmushi suka fara da sarawa Zarah. Kallon Ahmad tayi sai kuma ta kau da kai da sauri idanuwanta a k'asa ta ce"Ai haka ne ko?" Ta fad'a k'irjinta na bugawa saboda kar ya gwalasheta, zai yi magana Usman ya rigashi daccewa"Naganarta haka ne kuma ni na baku tabbaci." Wani sanyi Zarah taji yayin dasu suka fara ihuw da cewa sun fasa suka shige gidansu Zarah domin su jira zuwanta ta musu k'arin bayani. Ahmad cikin fushi da takaici ya ce"Baki da hankali? Kin san koni waye kike wannan maganar?" ta ce"kayi hakuri don Allah ni ban fad'a da wata manufa ba ina so su yarda dani ne domin subar k'udirunsu." Cikin d'aure fuska da masifa ya ce"Ƙudirinsu na banza da wofi wallahi zan d'au mummunan mataki a kan ki!" ta ce"Am...!" Katseta ya yi"Yi min shuru sakarya daƙiƙiya kawai!" Ya wuce mota. Hawaye taji na bin kuncinta Usman ya ce"Ki yi hakuri Zarah komai zai wuce amma me yasa kika ce musu haka?" ta ce"Wai an sasu satar k'uriyar za'be ne wai ba'aso ko mai abaya yaci kowa shine akace suje su sace ni kuma nace idan basu sace ba zan ba su aikin yi saboda mai arziki da mulki zan aura basu yarda ba suka biyoni shine na had'u daku nace haka." Sosai yake kallonta kamar idanuwansa zai fito ya ce"kKin san waye mai abaya?" Girgiza kanta tayi alamar a'a ta ce"Ni ban san shi ba na dai san yana takarar gwamnan jahar nan." Ajiyar zuciya ya saki ya ce"Haka ne, abin da kika yi kin kyauta sosai kuma tukwicinki mai tsoka ne." Ta ce"Wanne irin tukwici kuma?" Zai yi magana Ahmad ya banko k'ofar motar a fusace ya fito "Ka ga Malam idan bazaka shugo ba zan wuce" Usman ya ce"Zarah ki koma gida" Hannu yasa aljihu ya d'auko wasu kud'i masu yawa ya ce"Wannan kud'in ki rabawa matasan can sannan ki ba su tabbacin zasu sami aikin yi kar ki ji komai idan na sami lokaci zan dawo" Har zai shiga mota ta ce"uhmm tare zaku dawo dashi" Murmushi ya yi ya ce"Shi wa?" Ƙasa tayi da kai tana murmushi shima cikin dariya ya ce"Karki damu tare zamu dawo" Cike da murna ta shiga gida" Direba ya jasu suka bar unguwar saboda takaici Ahmad ko magana ya kasa yi idan ya tuno abin da Zarah tayi ya ja tsaki ya furta jahila kawai Usman na jinsa bai tanka masa ba. Ganin kud'in da Zarah ta raba musu suka k'ara yarda tabbas shid'in Zarah zata aura. Wani daga cikinsu ya ce"Nifa mutumin nan gani nake kamai Ahmad mai abaya ne" suka ce"Kai Baabaa sai kace baka da ido mai zai kawo mai abaya wannan unguwar karka mance da matsayinsa mana" Da haka suka banzatar da maganar domin ba sosai suka kallesa ba kuma sun yi shaye-shayensu ba lallai su gane ba, da haka wannan taro ya watse. Zarah ta shige d'aki tana jin farin ciki sosai take jin Ahmad cikin zuciyarta sai murmushi take da ta tuno fuskarsa da haka ta tashi ta d'auro alwala tayi sallah Feesu ta fice ita kuma bayan tasha kankana da lemun da ta siyo ta gyara kwanciya don bacci take ji sosai. _Zarah"Zarah"Zarahta me yasa kika bari wannan mutumin ya shiga zuciyarki kinsan ko shi waye kuwa?Zarahta me yasa kwana biyun nan ki ka mance dani saboda tafiyar da nayi to gani na dawo gare ki Zarahta kuma babu wani da ya isa ya shiga tsakanina da ke._ Muryar Hisham taji cijin masarrafar sautinta. Yana faɗa cikin sautinsa mai amsa kuwwa! Da sauri ta fara waige-waige........✍️ *Last free pages ya ƙare a 20 ƴar uwa hanzarta saya kar ayi babu ke, gawurtattu biyar tafiyar ta musammance. 08104335144* Fatima Rabiu Sunusi 0037219728 StanbicIBTC Bank. Shaidar biya tanan ?? 0810 433 5144